Sanata Natasha na tsoron dawo wa Nijeriya don kada a kama ta – Rahoton NPN

Daga BELLO A. BABAJI

Sanatar da aka dakatar a Majalisar Dattawan Nijeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan tana tsoron dawo wa Nijeriya, bayan kalaman da ta yi a zaman Majalisar Dokoki ta Duniya (IPU), kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta ruwaito.

Wasu makusanta ga sanatar sun ce tana tsoron za a kama ta matuƙar ta dawo Nijeriya.

A ranar 12 ga watan Maris ne Natasha ta halarci zaman, wanda aka yi a New York, inda ta koka game da batun dakatar da ita, ta na mai cewa an yi hakan ne don a rufe mata baki akan zargin da ta yi na cin zarafin ta a majalisar dattawan.

Ta kuma ce, an dakatar da ita ne a majalisar ba bisa ƙa’ida ba.

Lamarin ya biyo bayan dakatar da ita na watanni shida da majalisar ta yi bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa na.

A halin yanzu, hukumomin tsaro na DSS da NIA suna gudanar da bincike akan sanatar da yadda ta kutsa taron na IPU.

Jagoran sanatoci, Opeyemi Bamidele ya ƙalubalanci halaccin zuwan Natasha taron alhalin tana mataki da dakatarwa kuma ba tare da sahalewa ba a hukumance.

Ya ce, halartar taron sai da amincewar majalisa ba kawai daga waɗansu mutane na daban ba, sannan akwai ƙa’idojin halartar taron daga IPU.

Ya kuma ce, zuwan nata da yin magana a madadin ta ba wakiltar Nijeriya ba, shi ma wani abu na zargi.

Haka ma, Shugaban kwamitin Majalisar Dokoki na ƙasashe a Majalisar Dattawan, Sanata Jimoh Ibrahim, ya ce bai amince wa Natasha zuwa taron a matsayin wakiliyar Nijeriya ba.

Saidai, Lauyan kare haƙƙin ɗan-adam, Femi Falana ya yi gargaɗi akan duk wani bincike na musamman da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin yi akan yadda Natasha ta halarci zaman na IPU.