Majalisar Dokoki ta Ribas na shirin tsige Gwamna Fubara

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fitar saƙon gargaɗi bisa zargin rashin tsare aiki akan Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu, wanda hakan wani mataki ne na shirin tsige shi.

Guda 26 daga cikin ƴan majalisar suka watsa batun zargin a wata takardar sanarwa da aka aika wa Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, inda suka ce sun ɗauki matakin ne la’akari da taka sashe na 188 na dokar ƙasa na 1999 da wasu dokoki.

Ƴaƴan majalisar sun zargi Fubara da ɓarnatar da dukiyar jihar da kashe-kashe ba bisa doka ba, da hana ruwa gudu a Majalisar Dokokin da kuma yin wasu naɗe-naɗen jami’an gwamnati ba tare da tantancewa ba.

Sauran ababen da suka zargi gwamnan a kai sun haɗa da ƙwace kuɗaɗen albashi da alawus da wasu waɗanda majalisar ce ke da alhaki akansu da kuma na Akawon majalisar, Emeka Amadi.

Haka kuma, sun zargi mataimakiyar tasa da tallafa wa naɗa jami’an gwamnati ta haramtattun hanyoyi tare da kauce wa tantance su.

Tuni Kakakin majalisar, ya aika wa gwamna Fubara saƙon, inda ya ce aƙalla an samu sama da kaso ɗaya cikin uku na majalisar da suka tada batun zarge-zargen a kansa da mataimakin nasa, inda ya nemi gwamnan da ya kare kansa daga zargin da ake masa cikin kwanaki 14 kamar yadda doka ta tanadar.