Sarkin Daura: Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin bincike kan zargin cin zarafin ‘yar yawon buɗe ido

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina,ta bayyana matuƙar damuwa da takaici kan zargin cin zarafi da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya shafi Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, da wata mata mai yawon bude ido yar ƙasar waje.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Salisu Bala Zangon ya fitar da sanarwar haka,yace gwamnatin jihar ta ɗauki zargin da muhimmanci. Saboda haka, Gwamna Raɗɗa ya ba da umarnin kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da ba gwamnati shawara kan abin da ya dace.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta kuma dakatar da dukkan ayyukan fadar da tafiye-tafiyen Sarkin .

Gwamnati na tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da adalci, kuma za a aiwatar da sakamakon binciken kwamitin da shawarwarin da ya bayar gaba ɗaya.

Saboda haka, gwamnati na kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa, su bi doka, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

By ukarofi

Leave a Reply