Sarkin Musulmi ya ƙarfafi Qausain TV su ƙara himma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya shawarci Kamfanin Talabijin na Qausain TV da ya ruvanya ƙoƙarinsa wajen isar da saƙo ga al’umma.

A ziyarsar da Qausain TV ƙarƙashin jagorancin Shugaban Tashar, Nasir Musa Albanin Agege a fadar Sarkin Musulmin, ta ƙunshi wasu daga cikin shugabannin kamfanin da suka haxa da Auwal MB, Hashim Abubakar Musa, Khalifa Muhammad Babandede da kuma Hassan Haruna.

Bayan kyakkyawar tarba da tawagar ta samu, kazalika Sarkin Musulmin ya bulaci Qausain TV da ya ci gaba da aiki tuƙuru bisa ƙwarewa da sanin makamar aiki kamar yadda aka san shi wajen wayar da kan al’umma da ilmantar da su a yayin shirye-shiryensu.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kuma yaba da yadda tashar ke yaɗa shirye-shiryenta a bisa harsuna guda uku da suka haɗa da Turanci, Hausa da kuma Larabci.

A cikin jawabinsa a  yayin ziyarar, Shugaban Kamfanin Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Albanin Agege ya gode wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar bisa shawarwarin da ya ba su da kuma kyakkyawar tarbar da suka samu.

Ya kuma ƙara da cewa, “za mu fara aiki da shawarwarin da suka fito daga uba kuma jagora anan take wajen yaɗa shirye-shiryenmu a kowane lokaci.” 

Kazalika tawagar ta karrama Mai Alfarma Sarkin Musulmin da lambar yabo sannan ta miƙa masa kyautar hoton girmamawa na gilashi wanda ke ɗauke da hoton Sarkin Musulmin.

Daga ƙarshe tawagar ta samu damar yin hoto na jam’i tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da wasu daga cikin ‘yan majalisarsa.