Sayarwa Taiwan makamai yana nuna cewa Amurka ce babban tushen tayar da rikici a duniya

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan, hukumomin Amurka sun yanke shawarar sayar da fasahohin makamai masu linzami na Patriot, waɗanda suka kai darajar Dalar Amurka miliyan 95 ga yankin Taiwan na ƙasar Sin. Wannan dai shi ne karo na uku da Amurka ta sayar wa Taiwan makamai, tun bayan da gwamnatin Amurkan mai ci a yanzu ta hau karagar mulki, kuma watanni biyu kacal ke nan tun bayan karo da ya gabata. Halin da take yi na sayar da makamai ga Taiwan akai-akai, ya nuna tunanin Amurka na hura wuta, da rashin amincewa, da tsoron cewa duniya ba za ta kasance cikin ruɗani ba.

Me ake kawo wa Taiwan sakamakon sayen makamai daga Amurka? Mazauna yankin ne kawai za su iya fahimta. Wasu masu amfani da yanar gizo sun yi nuni da cewa, “Amurka ba ta son zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan”, kuma “Amurka ta kutsa kai ne don sake janyo kuɗi.” Wannan ya bayyana sosai, makircin siyasar Amurka na tayar da tarzoma, da yankar Taiwan a matsayin tunkiya mai ƙiba, da wadatar da masana’antun aikin sojan ta.

An amince cewa ƙasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na ƙasar Sin, wannan tarihi ne na haƙiƙanin gaskiya, wanda ba za a canja shi ba. A haƙiƙa dai, tsaron Taiwan ya dogara ne kan ci gaban dangantakar dake tsakanin gaɓoɓi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, ba wai sayen makamai daga Amurka ba.

Fassara: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *