Sin ta zama zakaran gwajin dafi a fannin tallafa wa sassan ƙasa da ƙasa

Daga CMG HAUSA

A duniyar yau mai cike da sauye sauye, ƙasashen duniya na ci gaba da kyautata hadin gwiwa, tare da faɗaɗa manufofin su na cuɗanya da ƙasashen waje. Bisa shaidu na zahiri, muna iya cewa ƙasar Sin na cikin ƙasashe ƙalilan dake samun ƙarin martaba a fannin sauke nauyin dake wuyan ta, game da tallafa wa sauran ƙasashen duniya, ƙarƙashin managartan manufofin ta na waje, da sauye sauye da take gudanarwa daidai da zamani.

Ƙasar Sin ta zama wani misali, na irin burin da ake da shi game da tallafa wa ƙasashe musamman masu tasowa, domin kawar da ƙalubalen bai ɗaya dake addabar duniya, da kuma haɗe sassan tattalin arziki domin moriyar kowa da kowa.

Ko shakka babu, cikin shekarun baya bayan nan, babbar manufar nan ta gina al’ummar duniya mai makomar bai ɗaya, da faɗaɗa tattaunawa, da cin moriyar juna tsakanin sassan al’ummun duniya, ta samu gagarumar nasara, inda manufar ke agazawa ci gaban duniya, da taimakawa ƙasashe masu rauni.

Ƙarƙashin manufofin hangen nesa na shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da jagorancin jam’iyyar Kwaminis mai mulkin ƙasar, na gudanar da ayyukan da suka kamata bisa tsari, da sauye sauye a fannonin raya tattalin arziki, da kyakkyawan salon siyasa, Sin ta samar da wani dandali na haɗe sassa daban daban, ta kuma faɗaɗa tallafin ta ga sauran ƙasashe mabuƙata, ta dukkanin hanyoyi gwargwadon ikon ta.

Tallafin jin kai da Sin ke samarwa ƙasashe, ya haifar da babban tasiri a shekarun baya bayan nan, inda Sin din ke haɗa ayyukan jin kai da hadin gwiwar samun bunkasuwa tare. Ƙarƙashin hakan, Sin ta tallafawa kasashe sama da 50 da alluran rigakafin cutar COVID-19, aikin da ya yi matuƙar samun yabo da jinjinawa daga al’ummun duniya.

Kazalika, Sin ta yi rawar gani wajen ba da agajin kawar da manyan ƙalubale da duniya ke fuskanta, kamar fannin sauyin yanayi, da hada hadar cinikayya, da raya tattalin arziki, da ƙara kyautata harkokin diflomasiyyar kasa da kasa.

A ‘yan kwanakin baya ma, Sin ta gudanar da jerin tarukan ƙasa da ƙasa, tare da abokan hulɗar ta na shiyyar da take a birnin Tunxi, na lardin Anhui, inda sassan suka tattauna batutuwa da suka jibanci raya tattalin arziki, da samar da tallafin jin kai ga makwafciyar ta Afghanistan.

Fassara: Saminu Alhassan