Shahararren shiri mai dogon zango na Labarina ya kusa dawowa

Daga AISHA ASAS

Shahararren fim ɗin nan mai dogon zango na Labarina ya kusa dawowa ga masu kallon finafinan Hausa a Nijeriya da ma ko’ina a faɗin duniya, inda za a fara zango na 5 da kuma na 6 a jere.

Darakta kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Aminu Saira, ne ya wallafa hakan a farkon makon nan ta kafafen sadarwarsa na zamani, inda ya bayyana cewa, tun da fari kamfanin Saira Movies ya tsara fara sake nuna fim ɗin ne a ƙarshen watan nan na Yuli, amma sakamakon rashin lafiya da wasu daga cikin jaruman fim ɗin guda biyu suka samu da kuma wasu matsaloli, waɗanda bai bayyana su ba, aka ɗage fara haska fim ɗin har sai zuwa cikin watan Agusta.

Idan dai za a iya tunawa, a watan da ya gabata aka sanar da fara ɗaukar shirin a birnin Kano, inda hotunan wajen ɗaukar shirin suka fantsama a kafafen sadarwa na zamani.

Jim kaɗan bayan hakan ne, Darakta Saira ya sanar da aniyar kamfanin na fara nuna shirin a cikin watan Yuli. To, amma wannan sabuwar sanarwar ta nuna cewa, a yanzu hakan ba zai yiwu ba kenan.

Shi dai shirin Labarina mai dogon zango ya samu matuƙar karɓuwa ga ma’abota kallon finafinan Hausa, wanda aka nuna kashi na 1 da na 3 da na 4 a tashar Arewa 24. To, sai dai kuma Malam Aminu Saira, kamar yadda aka saba kiran sa da sunan Malam, bai bayyana a tashar da za a kalli kashi na 5 da 6 biyar.

Idan dai za a iya tunawa, gabanin nuna kashi na 3 da 4 a shekara ta 2021 an yi yaɗa jita-jitar cewa, ba a tashar Arewa 24 za a cigaba da nuna shi ba, to amma sai kwatsam aka nuna shi ɗin a tashar.

Daga dukkan alamu dai, ko ma dai a wacce za a nuna shirin, ya samu karɓuwar da ma’abota kallon finafinan Hausa za su so su kalla ko a yaya ne.

Yanzu dai ma’abota kallon fim ɗin na Labarina sun duƙufa wajen zura idanu, don kashe ƙwaƙwatar idanunsu da zarar an fara nuna shi a nan gaba.