Buhari ya bai wa Ministan Ilimi wa’adin makonni 2 ya warware yajin aikin ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da ya warware yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) suka daɗe suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karɓi bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin jami’o’i.

Idan dai za a iya tunawa, ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta shiga yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran ƙungiyoyin ma sun janye aikinsu bayan hakan sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan buƙatunsu.

Sauran ƙungiyoyin uku da suka fara yajin aikin sun haɗa da manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya, SSANU, ƙungiyar ma’aikatan da ba na ilimi ba, NASU, da kuma ƙungiyar malaman fasaha ta ƙasa, NAAT.

Shugaba Buhari ya kira taron na ranar Talata domin karɓar bayanai daga tawagar gwamnati kan yajin aikin ya ɗauki tsawon lokaci ana yi.

Shugaban bayan jin ta bakin masu ruwa da tsaki na MDA da abin ya shafa ya umurci Ministan Ilimi da ya tabbatar da cewa an warware matsalar cikin makonni biyu tare da kawo masa rahoto.

Majiyoyi a taron sun kuma ce shugaba Buhari ya ba da umarnin cewa ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya kasance a duk wani taron da za a yi domin warware rikicin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, ya kamata sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha ya kasance cikin tawagar da za ta tunkari ƙungiyoyin da ke yajin aikin.

Daya daga cikin majiyoyin, ta ce shugaban ƙasar ya yabawa Ngige a ƙoƙarin da ya yi na kawo ƙarshen takun saƙa.