Sharhi: Amurka na sharɓar romon yaƙi yadda take so

Daga CMG HAUSA

A ‘yan kwanakin baya, Amurka ta fitar da kasafin kuɗin ta na shekarar 2023, mai kunshe da buƙatar bunƙasa kasafin ayyukan soji. Da ma dai kaso mai tsoka na kasafin kuɗin Amurka na fannin ayyukan soji, suna tafiya ne a ayyukan soji da take gudanarwa a ƙetare.

Bayan yaƙin duniya na II, Amurka ta shiga yaƙin Korea, da na Vietnam, da na yankin Gulf, da na Afghanistan da Iraƙi. Ana ma iya cewa cikin kusan ƙarni 2 da rabi tun bayan kafuwar ƙasar, shekaru 20 ne kadai kasar ta Amurka ba ta cikin yaƙi. Amurka ta kan shiga yaki kai tsaye, tana taimakawa masu aiwatar da yaƙin, tana kuma ingiza masu adawa da gwamnatoci su yi fito na fito da mahukunta, ta hanyar samar masu da makamai da harsasai.

A wasu lokutan kuma, tana horas da dakaru masu yaƙar gwamnatin ƙasashe, don haka a iya cewa, Amurka ta kafa tarihin tsoma hannu cikin al’amuran ƙasashe masu tarin yawa. Tun daga ƙarshen yaƙin duniya na II a shekarar 1945 zuwa 2001. Cikin tashe tashen hankula 248 da suka wakana a yankunan duniya 153, Amurka ce ta rura wutar 201 daga cikin su.

Abun tambaya shi ne, me ya sa Amurka ke matuƙar son yaki? Amsa ita ce, baya ga burin ta na yin babakere a duniya, tana kuma neman cimma muradun manyan kamfanonin sarrafa makamai nata, waɗanda rundunar sojin ƙasar, da dillalan makamai, da ‘yan siyasar ƙasar ke goyawa baya.

Idan har babu yaƙi, dole ne Amurka ta bullo da wani, domin wanzar da ribar da wadannan manyan kamfanonin makamai ke kwaɗayi, yayin da sauran sassa masu cin riba daga yakin ke jiran nasu kason.

Mai zane: Mustapha Bulama