2023: APC za ta bai wa mata kyautar fom

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa ya fitar da fom ɗin tsayawa takara a kyauta ga mata masu neman tsayawa takara a zaɓe mai zuwa na 2023.

Da ta ke jawabi a taron manema labarai a ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, sabuwar zaɓaɓɓiyar shugabar mata ta ƙasa, Betty Edu, ta ce, an cimma wannan matsayar ne domin ƙarfafa gwiwar duk mata masu neman takata.

Ta yi kira ga ɗaukacin matan Nijeriya da su zo jam’iyya mai mulki domin cin gajiyar wannan sabon salo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *