Sharhin littafin ‘Sin is a Puppy’ (Alhaki Kuikuiyo) daga Janine, Baturiyar Jamus

“A matsayina na Bajamushiya faɗan Rabi da Delu a littafin ya sani nishaɗi”

Daga JANINE DRAEGER (TALATU)

Taƙaitaccen bayanin littafin:
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ita ce marubuciyar littafin ‘Sin is a Puppy’, wanda asali a cikin harshen Hausa aka rubuta, mai suna ‘Alhaki Kuikuiyo’, kuma aka fassara zuwa harshen Ingilishi. Ramat General Enterprise ne suka wallafa a shekarar 1990. Farfesa Aliyu Kamal ne ya yi fassara zuwa harshen Ingilishi, kuma an wallafa wannan a Blaft Publications, cikin birnin Chennai a Ƙasar Indiya a shekarar 2012. Wannan ne fassarar da aka yi na wannan littafi a karon farko, zuwa harshen Ingilishi.

Wannan labari yana magana ne a kan wasu iyalai da suke zaune a cikin birnin Kano, kuma a cikin wannan labari akwai jigogi na soyyaya, nuna adalci, haƙuri, da imani da Allah.

Labarin an gina shi ne, a kan wata jaruma, mai suna Rabi da iyalinta. Tana da babbar ‘ya mai suna Saudatu, haka kuma sunan mijinta Alhaji Abdu. 

Alhaji Abdu yana da rufin asiri, wato yana da kanti a Kasuwar Sabon Gari. Duk da yana da arziki na rufin asiri, ba ya taimaka wa iyalinsa wato dai suna shan wahala. A gidansa akwai matsalar rashin abinci, kuma yana cin zarafin matarsa Rabi. Rabi dai, ta haifa masa yara tara, kuma sa’annan tana kula da Ladidi, ‘yar matar Alhaji Abdu wacce ya saka.

Wata rana, Alhaji Abdu ya gamu da Delu, tsohuwar karuwa, suka fara soyayya, har ya aure ta. Ya kashe kuɗi da yawa wajen neman ta, kuma ya fi nuna mata so, fiye da Rabi da ma yaransa. Wata rana, bayan Sa’adatu ta dawo daga makaranta, ta tarar ana rikici a cikin gida, wato a tsakanin Rabi da Delu. Hakan ya kai ga Alhaji Abdu ya saki Rabi. 

Rabi dai, ta samu kanta cikin matsananciyar wahala, ga yara, kuma ba ta samun wani taimako daga Alhaji Abdu. 

Bayan ‘yan watanni, Saudatu ta yi kiciɓis da Alhaji Abubakar Barau. Ya nuna yana sonta, ya je neman auren ta. Maimakon Alhaji Abdu a matsayinsa na mahaifi, ya kula, sai ya ƙi taimaka wa ‘yarsa a kan sha’anin maganar auren da sayen kayan ɗaki. Duk da haka, da taimakon ɗan’uwansa Alhaji Bello da ɗan‘uwan Rabi, mai suna Malam Shehu, aka yi sa’a komai ya tafi daidai, wato Alhaji Abubakar da Saudatu suka yi aure.

Saudatu dai ita ce ta uku a gidan Alhaji Abubakar. Babbar matsalar da aka fara samu ita ce, ta zamantakewa a tsakanin matan, wato dai matansa ba su da haɗin kai. A cikin wannan yanayi ne na hargowa da rashin zaman lafiya, Alhaji Abubakar ya saki uwargidansa Hajiya Amina. Ita kuwa ta biyu, mai suna Hajiya Halima, ta ci gaba da gallaza wa Saudatu. Daga ƙarshe dai, ita ma Hajiya Halima ta bar gidan, sai aka bar Alhaji Abubakar da Saudatu, suka zauna cikin farin ciki.

Wata rana ibtila’i ya auka wa Alhaji Abdu. Gobarar da aka yi a Kasuwar Sabon Gari, ya ritsa da kantinsa, komai ya ƙone ƙurmus. Bayan haka, ‘yar motar da yake ji da ita, aka zo aka sace. Wannan lamari sai da ya jefa Alhaji Abdu kwanciya a gadon asibiti, wato ya yi rashin lafiya. Bayan an sallame shi ne, da ya dawo gidansa, sai ya kama matarsa Delu, tare da wani saurayi. Nan ma ya sake ta.

Komai ya rincave masa, babu mota, babu kuɗi, kuma babu iyali. Haka dai, ɗan’uwansa Alhaji Bello ya lallashi Rabi da ta dawo gidan tsohon mijinta. Rabi ta koma, amma ta zama ita ce uwa, ita ce maɗaukiya a cikin gidan. Ita ce take kula da sha’anin cikin gida, ta gyara gidan sosai, abubuwa suka zama suna tafiya yadda ya kamata. Shi kuwa Alhaji Abdu, Allah Ya taimake shi ya canza halayensa. Cikin ikon Allah, surukinsa Alhaji Abubakar ya buɗe wani kanti a Kantin Kwari, kuma ya ɗaura Alhaji Abdu a kai.  

Sharhi:
Wannan littafi da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ta rubuta, tana son ta nuna cewa, idan miji ko mata suna da kirki da tsoron Allah, Allah zai taimake su, kuma a ƙarshe za su samu farin ciki da arziki.

Idan aka duba yadda aka shimfiɗa wannan labari, za a ga Alhaji Abdu ya tozarta matarsa ba gaira ba dalili, duk da arzikinsa, a waje yakan kula da kansa, ta hanyar sayen abinci mai daɗi ya ci, amma ya bar iyalinsa da yunwa. Wannan lamari ya fito da irin halayyar wasu mazaje ne da ba su kula da gidajensu, kuma yin hakan, abu ne maras kyau, kuma ba zai kai mutum ga gaci ba. 

Haka kuma, a cikin labarin, an nuna cewa, Alhaji Abdu ya ƙi ya yi komai a lokacin auren ‘yarsa, sai ma aka bar komai a wuyan Rabi da Alhaji Bello da Malam Shehu. A nan, ana nuna cewa ya kamata mahaifi ya san cewa, haƙƙin yaran da ya haifa yana wuyansa, kuma ƙin kula ɗin, abu ne mai muni. Ita Saudatu, Allah Ya sa mahaifiyarta da ‘yan’uwa sun taimaka an yi mata aure, amma a zahiri, idan mahaifi bai kula ya rufa wa ‘yarsa asiri ba, sai rashin kula ɗin ya iya jefa ‘ya mace cikin wata masifa.

A sha’anin zamantakewa ta aure, yana da kyau maigida ya riƙe gidansa, musamman ya yi ƙoƙari ya ga ya tabbatar da adalci a tsakanin matansa. Amma idan aka duba, za a ga cewa, Alhaji Abdu a cikin labarin, bai nuna adalci ba a tsakanin Rabi da Delu. Wannan abu mai muni ne, don ya nuna rashin tsoron Allah. Sai ga shi a ƙarshe, ya rasa duk arzikinsa da jarinsa, har da lafiyarsa.

Rabi da ‘yarta Saudatu, ta wani ɓangaren kuma, sun zama masu kirki da haƙuri a lokacin wahala, ko kuma a lokacin da aka jarrabe su, har ya kai ga Rabi ta mallaki gidan Alhaji Abdu.

Delu kuwa, dole ta bar gidan, bayan an kama ta tare da wani kwarto. Delu mace ce maras kunya, kuma a ƙarshe, halinta ya cutar da ita. 

Wannan labari ya nuna cewa, akwai bambanci sosai a tsakanin gaskiya da ƙarya, da tsakanin abu mai kyau da maras kyau. Haka ma ya fito fili a cikin gidan Alhaji Abubakar da matansa, wanda a ƙarshe suka bar wa Saudatu gidan. Saudatu kuma, saboda kirkin ta, ta kula da yaransu tamkar nata.

Duk da dai wannan ƙagaggen labari ne da aka rubuta, don nishaɗi, amma akwai darussa da dama da za a iya ɗauka a ciki, waɗanda suka haɗa, haƙuri, son Allah da imani da Shi, juriya, kyautatawa, aikata aikin alheri, da dai sauransu.

Cikin littafin, akwai abubuwan da suka faru, a matsayina na Bajamushiya, suka ba ni nishaɗi. Misali, inda Rabi da Delu suka yi faɗa har da doke-doke. Wannan ya ba ni mamaki, saboda yadda aka faro labarin, an nuna Rabi ba za ta iya irin wannan hali ba, saboda kamalarta, amma sai ga shi, watakila ko dai an ƙure haƙurin ta ne, ita da Rabi suna ta gwabzawa.

 

Marubuciyar littafin ‘Alhaki Kuikuiyo’, Hajiya Balarabs Ramat yakubu

Haka kuma akwai babi guda da aka keve ana bayani a kan iyayen Alhaji Abubakar. Duk da dai ya ba ni sha’awa, saboda an yi nuni na soyayya a tsakanin iyayensa, akwai kuma maganar tsibbu, kuma an gina don a nuna tushe da asalin Alhaji Abubakar ne, amma shafukan sun yi yawa, musamman idan aka yi la’akari da cewa, shi Alhaji Abubakar ba shi ne jigo a littafin ba.

A ra’ayina, zan fi son na ji an yi bayani a kan iyayen Rabi ko Alhaji Abdu, tun da su ne jigogi masu ƙarfi a cikin labarin. Wato abin nufi a nan shi ne, zai kyautu a san wani rin rayuwa Alhaji Abdu ya taso a ciki, har ya zama maras halin kirki, amma kuma ɗan’uwansa Alhaji Bello mutumin kirki ne. 

Haka kuma, zai yi kyau mu san mene ne ya faru, har aka nuna rashin kirkin matan Alhaji Abubakar, wato Hajiya Amina da Hajiya Halima. Dalili kuwa shi ne, labarin ya fifita Saudatu a kan sauran mata, duk da su ne suka riga ta shiga gidan Alhaji Abubakar.

A batun nata hali na kirki ko akasi, wannan labari ya fito da mata da dama marasa hali na kirki, amma a fannin maza kuma, Alhaji Abdu ne kawai, mai mummunan hali. Duk da dai littafin ya nuna wahalar da mata sukan iya shiga, misali idan muka duba rayuwar Rabi, amma ta wani ɓangaren kuma, an nuna mafi yawan misalai marasa kyau daga mata ne. Ƙarshen labarin ɗan’uwanta Malam Shehu da surukinta Alhaji Bello, sun sa Rabi ta dawo gidan Alhaji Abdu, duk da yake ba ta son sa. Littafin ya tabbatar cewa, mu mata, muna rayuwa ne a cikin duniyar maza.

Janine Draeger (Talatu):
Janina Draeger ta girma a birnin Luebeck, a Ƙasar Jamus ta Arewa. Ta fara koyon harshen Hausa a Jami’ar Leipzig a ƙarƙashin Malamin Hausa mai suna Dr. Ari Awagana, a cikin shekarar 2016. A shekarar 2018/19 ne ta je Kano, ta yi nazarin Hausa a Jami’ar Bayero, Kano. Yanzu tana yin Digiri na biyu a Jami’ar Hamburg, a fannin harsunan Afirka, kuma tana ɗaukan darussan Hausa tare da Malama Dr Umma Aliyu Musa.