Basir da yadda ya ke shafar zamantakewar ma’aurata

Daga BILKISU YUSUF ALI

TAMBAYA:
Anti Bilki, Ina so a yi min bayani ne kan mene ne ciwon basir kuma ya ake yi ya ke shafar zamantakewar ma’aurata?

AMSA:
Ciwon Basir wani ciwo ne kuma marar daɗi da ya ke addabar al’umma duk da da dama mutane kan yi masa wani kallo na daban wataƙila don yadda ake jingina kowanne ciwo da basur ne don haka ake masa kallon shu’umi ko kuma kowacce cuta daga gare shi take oho? Kalmar basir asalinta Balarabiyar kalma ce inda da Larabci ake kiranta Bawasir ko Basuur da Turanci ana kiransa da ( Hemorrhoid /pile) Ciwo ne da yake a dubura da kuma ciki in kuma ya gawurta yana iya taɓa dukkan gaɓɓai. Basur kan shafi kwakwalwa da tunanin ɗan’adam.

Dalilan da ke haifar da ciwon basur suna da yawa kwarai da gaske amma kuma kamar mafiya yawan cutoci sukan faru ba tare da wani dalili ba sai don ƙudira ta Ubangiji. Basur ciwo ne mai hatsarin gaske don yana cin jiki a sannu a hankula inda a ƙarshe in ya yi ƙarfi zai zama kuma maganin yana gagara ta ruwan sanyi ko a hankula.

Duk da masana sun ayyana wasu dalilai da kan haifar da ciwon Basur da dama amma za mu ɗau muhimman dalilan daga ciki kamar haka:-
-Ciye-ciye wanda suke gurɓata ciki wanda cikin bai amsa ba ko ci fiye da ƙima ko cin abinci mai tauri kuma ba tare da sirkawa da mai ruwa-ruwa wanda ka wahalae da uwar ciki/tumbi wajen narkawa.
-Cin abinci da zai ke haifar da ƙugin ciki kamar maiƙo da sauransu.
-Gajiyar jijiyoyin dubura sakamakon wahala da suke sha.
-Mata da dama kan haɗu da larurar Basur ta dalilin haihuwa ko don abin da aka riƙa ci a dalilin laulayi ko kuma don yawan yunƙurin haihuwa kafin haihuwa ta zo.
-Ga waɗanda ke zuwa ga iyalansu ta dubura ko kuma luwaɗI shi ma yana kawo larurar basur saboda kan janyowa dubura ta taɓu.
-Ga wanda ke yin bayan gida da kyar ko da tauri shi ma kan janyo Basur wannan yunkurin shi ke janyowa har baya yake fita.
-Yawan shaye-shayen magunguna na gargajiya ko ma na Baturen ba bisa ƙa’ida ba.
-Shan barasa
-Ƙiba

Nau’in Basur:
Manyan nau’ikan Basur manya guda biyu ne duk da Basir yana da salo daban-daban amma dai manyan sune
-Basur na ciki
-Basur mai zubar jini ko basur mai tsiro

Za mu ɗora a mako na gaba in sha Allah.

Ga mai tambaya ko neman ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin, amma tes kawai ko ta WhatsApp a 08039475191 ko a shafina na Facebook mai suna Bilkisu Yusuf Ali.