•Kotun ta yi fatali da shaidar takardun Chicago
•Ta raraki Peter Obi
•Tinubu ye nemi haɗin kai don gina Nijeriya
•Atiku da Obi su jira zuwa 2031, cewar Ganduje
•PDP da LP sun maida martani
•Buhari ya yi maraba da hukuncin
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun Ƙolin Nijeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.
Hukuncin na alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya ce, “a ƙarshe, bayan warware duk wasu lamurra game da ɗaukaka ƙarar, zan iya cewa babu hujjoji masu ƙwari game da ɗaukaka ƙarar, saboda haka an yi watsi da ita,”
“Hukuncin kotu ta baya da aka zartar a ranar 6 ga watan Satumba wanda ya tabbatar da nasarar wanda ake ƙara na biyu a matsayin Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya, an tabbatar da shi.”
Wannan dai ya kawo ƙarshen duk wata turka-turka game da batun nasarar da shugaban na Nijeriya ya samu a zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.
Kotun ta bayyana haka ne a hukuncin da ta zartar jiya Alhamis bayan ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyun adawa suka ɗaukaka kan hukuncin kotun ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.
Tun farko alƙalan kotun sun yi watsi da buƙatar Atiku ta gabatar da wasu ƙarin hujjoji kan cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaɓe ta INEC takardar kammala karatu ta bogi gabanin zaɓen Shugaban Ƙasa.
Atiku ya yi iƙirarin cewa takardun da Tinubu ya gabatar daga Jami’ar Jihar Chicago ta Amurka ba sahihai ba ne, sai dai bai samu gabatar da hujjojinsa ba a kotun ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.
Lauyan Atiku Chris Uche (SAN), ya ce takardar mai shafi 32 da aka miƙa wa wanda yake karewa ya kamata a shigar da ita domin a yi adalci.
Sai dai kotun ta yanke hukuncin cewa lokacin shigar da irin waɗannan shaidun ya wuce, saboda tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasar.
Wa’adin kwanaki 180 ya qare ne a ranar 17 ga Satumba, wanda hakan ya sa Kotun Ƙoli ba ta da hurumin karɓar takardar.
Haka zalika kotun ta yi watsi da ƙarar da Peter Obi na Jam’iyyar Labour ya shigar na ƙalubalantar zaɓen Bola Tinubu.
Kotun ta kuma ce a hukuncin da ta ɗauka na bai ɗaya ɗaya da ke cikin qarar da Mista Obi ya shigar, wato zargin da ake masa na tsayar da Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa da kuma yin takarar Sanata a zaɓen da aka gudanar a watan Fabrairu, tun da farko kotun ta warware shi ba zai yiwu a yi shari’a akan shi ba.
Kotun dai ta yi raga-raga da manyan hujjojin Atiku da Obi, inda ta yi filla-filla da hujjojin da ‘yan takarar na jam’iyyun adawa su ka gabatar wajen ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu.
Alƙalan sun haɗu a kan cewa babu inda doka ta wajabta samun kashi 25 na ƙuri’un Abuja kafin ɗan takara ya yi nasarar lashe zaɓe.
Abin da sashe na 134 na doka ta ce shi ne mai neman takara ya tashi da aƙalla kaso 25 a kaso biyu bisa uku na jihohi 36 da kuma Abuja.
Mai shari’a John Okoro ya rusa ƙarar Chris Uche, SAN a madadin Atiku Abubakar na cewa ba a aika sakamakon zaɓen ta na’ura ba. Kotun Ƙoli ta ce gazawar na’urar IREV ba ta nufin daina tattara sakamako.
Alƙalan da su ka yi hukuncin sun ce rashin aikin IREV ba zai yi sanadiyyar da masu kaɗa ƙuri’a za su samu wani rashin gamsuwa ba.
A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa da ta yi zaman ta a birnin Abuja ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar suna ƙalubalantar zaɓen na Shugaba Tinubu.
Sai dai rashin gamsuwa da hukuncin kotun ya sanya manyan jam’iyyun adawar da ‘yan takararta suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.
A lokacin ɗaukaka ƙarar, Atiku ya bijiro da sabbin tuhume-tuhume guda 35, da ke sukar hukuncin da kotun farko ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ta yanke.
A martanin da ya yi jim kaɗan bayan hukuncin Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu ya bayyana wa ‘yan jam’iyyun adawa cewa lokaci ya yi da ya kamata a taru a gina ƙasar Nijeriya tun da shari’ar zaɓe ta ƙare.
Ya ce kotu ta yi hukunci na adalci game da dukkan ƙorafe-ƙorafe ba tare da son kai ko kuma nuna tsoro ba yayin hukucin.
A cewarsa: “Na karɓi wannan hukunci da hannu biyu wanda Mai Shari’a John Okoro ya jagoranta bayan ƙorafi daga jam’iyyun PDP da LP na ƙalubalantar zaɓe na.
“Babu kokwanto wannan hukuncin kotu ya tabbatar da cewa dimukraɗiyya da kuma ɓangaren shari’a a ƙasar na ƙara samun ci gaba da kuma ɗorewa.”
Tinubu ya ce duk da barazana da wasu ‘yan siyasa ke yi wa ɓangaren shari’a musamman kan wannan hukunci, amma kotu ta yi hukunci na adalci.
Ya buƙaci sauran ‘yan siyasa da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe don gina ƙasar Nijeriya da kawo ci gaba.
Shi ma a martaninsa, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na tabbatar da zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shaida ce da ke nuna cewa ba a yi magudin zaɓen Shugaban Ƙasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu ba kamar yadda ‘yan adawa ke iƙirari.
A wata sanarwa a ranar Alhamis ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Edwin Olofu, Ganduje ya kuma buƙaci ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP da na Jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, da ya jira har zuwa 2031 lokacin da Tinubu zai kammala waa’adinsa na biyu.
Ganduje, wanda ya taya Tinubu murna, ya ce hukuncin ya koma kan duk wani iƙirari na jam’iyyun adawa.
Ganduje ya ce hukuncin Kotun Qoli zai ba Shugaba Tinubu damar mayar da hankali wajen aiwatar da ƙudirinsa na sabunta fanta wato “Renewed Hope” na jam’iyyar APC domin amfanin ‘yan Nijeriya.
Shugaban Jam’iyyar APC ya yi kira ga Atiku da Obi da su yi haƙuri su haɗa kai da Shugaba Tinubu domin sake dawo da ƙasar nan wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce, “Nijeriya ta mu ce ta mu baki ɗaya, haƙƙinmu ne a matsayinmu na ’yan kishin ƙasa mu haɗa dukiyarmu domin ciyar da ƙasa gaba. Ina taya Atiku da Obi murna bisa gwagwarmayar da suka yi na kare dimokuraɗiyya da doka.
“Wannan ita ce dimokuraɗiyya. Nasarar Tinubu wata nasara ce ga mulkin dimokraɗiyya a ƙasar. Har yanzu akwai sauran damar Obi da Atiku su tabbatar da aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa bayan wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a 2031.”
Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da siyasa ba, da su zu a gina tafi tare domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya samar da ribar dimokuraɗiyya da kuma ciyar da ƙasar nan kan turbar ci gaba mai ɗorewa.
A martanin da ta yi, babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce hukuncin Kotun Ƙoli a kan ƙorafin da ta shigar tare da ɗan takararta Atiku Abubakar, a kan nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban abin tayar da hankali ne.
Ta ce ‘yan Nijeriya har yanzu sun kasa fahimtar yadda kotun ƙoli ta lamunci manyan batutuwan yin jabun takardu da tafka karya da shaidar zur, bisa doron rashin cika ƙa’idojin shigar da ƙara.
Kotun dai ta yanke hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaɓen Tinubu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
PDP ta ce ita, da mafi yawan al’ummar Nijeriya sun kaɗu kuma sun ji takaici tare da nuna damuwa a kan tunanin Kotun Ƙolin, wanda jam’iyyar adawar ta ce ta yi imani ya saba da tanade-tanaden tsarin mulkin Nijeriya da kundin dokokin zaɓen ƙasar.
Sanarwar da sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Onarabul Debo Ologunagba ya fitar, babbar jam’iyyar adawar ta jaddada cewa wani abin takaici ne a ce kotun qƙoli ta gaza ɗabbaka tanade-tanaden doka.
A maimakon haka, sai ta yi watsi da kyakkyawan zaton mafi yawan al’ummar Nijeriya waɗanda ke kallonta a matsayin gidan samun adalci ta hanyar yanke hukunci a kan batun da ya yi la’akari da dokoki da al’amura na gaskiya a cikin wannan shari’a.
Ta ce da gaske ‘yan Nijeriya sun yi tsammanin kotun ƙoli za ta tabbatar kuma ta kare tanade-tanaden tsarin mulkin 1999 waɗanda suka fayyace ƙarara batun cancantar dan takara da sharaɗi mafi ƙaranci da ake buƙatar cikawa kafin a ayyana mutum a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar Nijeriya.
“Musamman la’akari da buƙatar doka ta cin kashi 25 na quri’un da aka kaɗa a birnin Abuja da kuma batutuwan da suka keta dokoki da tsare-tsaren zaɓe.”
PDP dai ta ci gaba da zargin jam’iyyar APC mai mulki da tafka almundahana da jirkita sakamakon zaɓe.
Ta kuma yi iƙirarin cewa hukuncin kamar yadda shaida ta bayyana, ya sanyaya ƙwarin gwiwar da ‘yan Nijeriya ke da shi ga ɓangaren shari’a, musamman a matsayinta kotun ƙoli na madafar ƙarshe ga talaka.
Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce matakin yin watsi da ƙararrakin da Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Mista Peter Obi na Labour da Kotun Ƙoli ta yi, wani abin farin ciki ne a gare shi da kuma mafi yawan ‘yan ƙasar.
Tsohon shugaban ƙasar ya sake maimaita abin da ya ce a kan hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa hukuncin da aka yanke abin yin maraba da shi ne “tabbatar da ra’ayin mafi yawan jama’a ba tare da ƙudurin son rai ba.
“Yanzu da muka isa tasha ta ƙarshe, bayan tafiyar watanni 8 na doka, al’umma ta cancanci hutu. ‘Yan adawa sun yi gwagwarmaya mai kyau. Kasancewar yanzu sun ƙwaci ‘yancinsu kamar yadda tsarin mulki ya ba su dama, ya kamata su ƙulla zumunci da gwamnatin APC ta Tinubu/Shettima. Su bar gwamnati ta tafiyar da mulkinta, jama’a su ci moriyar alƙawurran da Jam’iyyar APC ta ɗauka,” inji Buhari.
Ita kuwa, Jam’iyyar Labour, ta hannun shugabanta na ƙasa Julius Abure, ta yi Allah wadai da hukuncin Kotun Ƙoli, inda ta bayyana hukuncin a matsayin “gurɓata tsarin shari’a.”
Julius Abure, ya ƙara da cewa hakan ya nuna ƙarara cewa Nijeriya “ta nuna mulkin kama-karya.”
Ya bayyana fargabarsa dangane da yadda ɓangaren zartarwa ke ganin tasirinsa a ɓangaren shari’a da na majalisa.
Abure ya ƙara nuna damuwarsa kan yadda za a iya muzgunawa shugabannin jam’iyyar Labour, ciki har da shi da ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi.
Ya yi hasashen cewa irin waɗannan ayyuka na iya zama yunƙurin murƙushe jam’iyyar da manufarta na kawo sabuwar Nijeriya. Duk da koma bayan da kotun ƙolin ta samu, Julius Abure ya buƙaci mambobin jam’iyyar Labour da magoya bayan jam’iyyar da su yi taka-tsan-tsan tare da jajircewa wajen neman kyakkyawar makoma ga ƙasar.
Ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su tashi tsaye tare da ‘yan Nijeriya a ƙoƙarinsu na tabbatar da dimukraɗiyya.
