SHAROBA ta tallafa wa marayu a ɓangaren karatu

Daga MUHAMMADU MUJITABA, a Kano

Ƙungiyar tsofffin ɗalibai ta Sharaɗa ‘Old Boys Association’ (SHAROBA) Aji na 1991 ƙarƙashin shugabancin Malam Rabiu Hamisu Danjidda ta bada tallafin kayan karatu ga makarantar da suka kammala shekaru 30 da suka wuce.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin ɗaliban, Auwalu S Mu’azu, ya bayyana a lokacin taron da ƙungiyar ta gabatar a ɗakin taro na ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano a ranar Asabar da ta gabata.

Har ila yau, ya qara da cewa, baya ga tallafi ga makarantar haka kuma ƙungiyar tsoffin ɗaliban ta SHAROBA ta ga cewa da ta zaƙulo tsoffin ɗaliban da suka kwanta dama domin jaddada musu addu’a ta neman rahama da kuma neman kyautata ta mu bayan ta su wanda a haka ta zaƙulo tsoffin ɗalibai 30 wanda kuma aka zartar da cewa za a ziyarci iyalansu da ‘ya’yansu domin tallafa musu da kayan abinci da sutura na ɗan abin da ya sauƙaƙa domin rage musu raɗaɗi na rasa iyayensu wanda kuma hakan zai zama an ƙara sadar da zumunci a tsakanin tsofafin ɗaliban rayayyu da kuma iyalai da ‘ya’yan tsofafin ɗaliban da suka kwanta dama domin ci gaba da zumunci da tausaya musu.

Shi ma Alhaji Danlami Ali Aji na 1990, wanda ya yi Magana a madadin shugaban SHAROBA na ƙasa, Danlami Ali wanda shi ne sakataren ƙungiyar a matakin ƙasa ya ce, wannan ƙungiya tasu ta tattara ƙungiyoyin tsofafin ɗalibai tun Aji na 1984 har zuwa yau ko wanne mataki akwai shugabanci da suke yin taro kuma ana gayyatar mu domin tattauna matsaloli da cigaba da kuma yadda za a taimka wa makarantar wanda hakan ne ya sa kodayaushe tsofaffin ɗalibai ke ziyartar makarantar ko da yaushe.

A ƙarshe shugaban makarantar na yanzu Alhaji Ahmad Umar ya yaba wa tsofafin ɗaliban kan irin gudunmawar da suke bayarwa ga makarantar da kuma taimakon juna da suke yi inda kuma ya buƙaci tsofafin ɗaliban da ɗaukacin al’umma akan su tashi tsaye wajen kula da tarbiyar matasa domin ana cikin wani hali na lalacewar tarbiyar matasa a yau. Malam Adamu Arrow Ƙofar Nasarawa na daga cikin ɗalibai da su ka nuna farin ciki su a taran shuruba a aji na 1991.