Shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya riba ce ga ƙasashe masu tasowa

Daga SAMISU HASSAN

Yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da nazari, da fafutukar neman kyakkyawar makoma a wannan mawuyacin lokaci da duniya take ciki, musamman ta fuskar koma bayan tattalin arziki, da gurguncewar sassa daban daban na ci gaba, sakamakon bullar annobar COVID-19, da rikicin ƙasar Ukraine da suka haifar da mummunar illa ga duniya, a hannu guda, ƙasashe musamman masu tasowa, na da kyakkyawan fatan samun ci gaba da wadata, ƙarƙashin ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, bisa shawarar nan ta Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya wadda ƙasar Sin ta gabatarwa duniya.

Cikin irin waɗannan ayyuka da a yanzu haka ke daf da kammala, akwai ginin tashar teku mai zurfi ta yankin Lekki na jihar Lagos dake Kudu maso yammacin Najeriya, wadda ƙasar Sin ta tallafa wajen gudanarwa.

’Yan Najeriya da dama, da masana tattalin arziki a ƙasar, na jinjinawa ƙasar Sin, bisa aiwatar da wannan muhimmin aiki mai tarin alfanu, wanda zai faɗaɗa damar Najeriya ta karbar manyan jiragen dakon kayayyaki daga sassan duniya daban daban.

Aikin wanda zai lashe tsabar kuɗi har dalar Amurka biliyan 1.5, a yanzu ya kai kaso 95 bisa dari na kammala, ana kuma sa ran gama shi baki ɗaya zuwa ƙarshen shekarar nan ta 2022.

Tashar za ta haɗe da yankin ciniki cikin ’yanci na jihar ta Lagos.

Da zarar tashar ta kammala, za ta zamo ta 3 da Najeriya ke da su, baya ga tsoffin tashoshin ruwa masu karɓar jiragen ruwa guda biyu dake fama da cinkoso.

Saɓanin tsofannin tashoshin biyu, sabuwar tashar teku mai zurfi ta Lekki, za ta iya karbar kayan da yawansu zai kai na sama da manyan sundukan dakon kaya masu faɗin ƙafa 20 har miliyan 2.7 a duk shekara, kana tashar tekun mai zurfi, za ta samarwa Najeriya zarafin karɓar sundukan dakon kayayyaki daga 3,000 zuwa 20,000 a kullum, wanda hakan ya sanya tashar zama ɗaya daga ayyuka mafi muhimmanci da Najeriya za ta ci gajiyar su, ƙarƙashin shawarar Ziri Ɗaya da hanya Daya.

Ko shakka babu wannan muhimmin aiki ne da zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya ta fuskar samun karin haraji, da guraben ayyukan yi, da fadada damammaki na kasuwanci da cinikayya, baya ga rage tsadar kuɗaɗen fito, da kara zamanintar da salon ba da hidimomin shige da fice da tashar za ta yi a ƙasar irin Najeriya, wadda ita ce mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.