Kamfanin Sin ya kammala aikin gina tashar samar da lantarki ta Ruzibazi a Burundi

Daga CMG HAUSA

An yi bikin murnar kammala aikin gina tashar samar da wutar lantarki bisa ƙarfin ruwa ta Ruzibazi da kamfanin ƙasar Sin ya yi a ƙasar Burundi a ranar 6 ga wata.

Shugaban ƙasar Evariste Ndayishimiye ya halarci bikin, tare gabatar da jawabi, inda ya yabawa namijin kokarin da kamfanin ƙasar Sin ya yi wajen kammala aikin a kan lokaci.

Shugaba Ndayishimiye ya nuna jin daɗinsa ga ɓangaren ƙasar Sin, bisa haɗin gwiwar da take yi da ƙasar Burundi a fannonin samar da ababen more rayuwa da aikin gona, ya kuma yaba wa ƙasar Sin kan yadda ta shawo kan matsaloli da dama da annobar ta haifar, da kuma kammala aikin kamar yadda aka tsara.

A nata ɓangaren, jakadar ƙasar Sin dake Burundi Zhao Jiangping ta bayyana cikin jawabin da ta gabatar yayin bikin cewa, kammala aikin gina tashar Ruzibazi, zai kasance sabon mafari na haɗin gwiwa tsakanin Sin da Burundi bisa jagorancin “Ayyuka tara” na haɗin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

Ta ƙara da cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da tallafawa Burundi da sauran ƙasashen Afirka, wajen raya makamashi da ake iya sabuntawa don samun wadatar makamashi.

An fara aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ƙarfin ruwa ta Ruzibazi ne tun daga watan Oktoban shekarar 2018, kuma an kammala aikin gwajin na’urar ta ƙarshe, daga baya na’urori uku sun fara aiki a watan Yulin bana.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa