Shawarwarin masoyana ba sa canja min ra’ayi kan abin da zan rubuta – Ummu Maheer

“Masu karatu ba sa mana uzuri”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Ummu Maheer ko kuma Miss Green kamar yadda wasu suka fi saninta, na daga cikin matasan marubutan onlayin da Allah Ya tarfa wa garinsu nono, sakamakon yadda littattafanta ke samun karɓuwa a wajen masu karatu, har da tsakanin ‘yan’uwa marubuta. Shekaru biyar da fara rubutunta a zaurukan sada zumunta, Rabi’atu Bashir Abdullahi, kamar yadda asalin sunanta yake ta rubuta littattafai sun kai 19, yayin da take shirye-shiryen wallafa wasu a ciki. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba AbubakarYakubu, marubuciyar ta bayyana burinta na ganin marubuta sun haɗa kai wajen ƙalubalantar masu rubutun batsa, da ta ce suna ɓata wa sauran marubuta suna, a idon duniya. Ga yadda tattaunawar su ta kasance. A yi karatu lafiya. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki. Mene ne cikakken sunanki da abubuwan da ki ke yi na rayuwa?

MISS GREEN: Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Rabi’atu Bashir Abdullahi, wacce aka fi sani da Ummu Maheer ko kuma Miss Green, a cikin rubuce-rubucena. Ni marubuciya ce, duk da dai ba wani daɗewa na yi a harkar ba. Amma Allah Ya nufe ni da rubuta littattafai da gajerun labarai da dama. Sannan yanzu haka ina aiki da wata manhajar rubutun Hausa ta WikiHausa, inda nake aiki a fannin rubutu da tacewa. Har wayau kuma ni ýar kasuwa ce, ina siyar da atamfofi da kayan kicin. Ina kuma gyaran jiki na amare. Sannan ina yin sabulu na sayarwa, da man shafawa da man Kitso. 

Ina ki ka samu sunan Miss Green? Kuma me hakan yake nufi? 

Na samu sunan Miss Green ne tun a makaranta, saboda ni masoyiya launin kore ce . Shi ya sa na tashi har na girma da wannan sunan.

Shi kuma Ummu Maheer fa? 

Shi kuma suna ne da ya samo asali tun ina budurwa. Ni ce na sanyawa kaina wannan sunan saboda ina son sunan Maheer sosai. Cikin yardar Allah kuma har ni ma na samu nawa Maheer ɗin.

Gaya mana tarihin rayuwarki, da inda ki ka yi karatu.

An haife ni ne a Unguwar Daurawa, da ke yankin ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare a Daurawa Community, sannan na yi karatuna na matakin sakandire a makarantar nazarin harkokin kasuwanci, wato Kano School of Business Studies (KSBS). Sannan na yi karatu a Kwalejin Nazarin Harkokin Gona ta College of Agricultural Produce Technology Kano. Sannan kuma yanzu haka ina aikin koyarwa a makarantun, Islamiyya da na boko. 

Tun yaushe kika fara rubutun adabi? Kuma me ya baki sha’awa a rubutun labaran hikaya?

Na fara rubutun adabi a shekarar 2018. Sannan abin da ya bani sha’awa shi ne na daɗe ina son isar da saƙo musamman akan rayuwar mu ta yanzu, amma na rasa yadda zan yi. Sai daga bisani na ga ashe zan iya cimma burina ta wannan hanyar, don na isar da saƙon da nake son isarwa. Babu shakka abin da ya fi bani sha’awa akan harkar rubutun hikaya bai wuce yadda za ka isar da saƙon ka ta hanya sauƙaƙƙiya wacce mata bila’adadin za su karanta kuma su amfana.

Wanne labari ki ka fara rubutawa? Kuma wa ya fara koya miki yadda ake rubutun labari?

Labarin da na fara rubutawa shi ne ‘Uwargidana’, sannan ‘Nabila Dikko’, wata babbar marubuciyar onlayin, ita ce wacce ta fara koya min rubutun labari a onlayin. Sannan kuma sai Allah Ya haɗa ni da wata ‘yar baiwar marubuciya mai suna Hassana ɗanlarabawa, wacce ita ma gaskiya ta taimaka min sosai har Allah Ya kawo ni wannan lokacin, da ni ma nake jin kaina a matsayin marubuciya wacce za ta iya bada gudunmawa.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayen wasu daga cikinsu.

Na rubuta littattafai guda 19, daga cikinsu akwai; ‘Abin Cikin ƙwai’, ‘Silar Fyaɗe’, ‘Auren Dole’, ‘ɗinyar Makaho’, ‘Inda Ba ƙasa’, ‘Zulfah’, ‘Inayatullah’, ‘Darasi’, ‘Doctor Nawwara’, ‘A Sanadin Abayar Sallah’, ‘Basma’, ‘Akan Aikina’, ‘ɗan Halak’, da kuma ‘Farouk’. 

Ki gaya mana wasu darussa da ke ƙunshe a cikin wasu fitattu 3 daga littattafan da ki ka rubuta. 

To, da farko dai akwai littafin ‘Abin Cikin ƙwai’ wanda labari ne da yake ƙunshe da darussa akan zamantakewa, musamman irin ta zaman gidan miji, wato yadda mace za ta zauna da surukarta, a yayin da zaman gida ɗaya ya haɗa su ko kuma zaman nesa. Sannan harwayau littafin yana ankarar da mata illar bin bokaye.

Sai littafin ‘Facala’, shi kuma labari ne da ke koyar da ilimin zama da facala, wato matar ƙani ko wa. Yayin da shi kuma littafin ‘Darasi’ yake koyar da illar ɗorawa yara mata talla.

Kin taɓa wallafa wani daga cikin littattafanki ne? 

Ban taɓa bugawa ba, amma ina da shirin buga wasu kwanan nan, in sha Allahu. Ina jiran a kammala gyare-gyaren da ake yi ne.

Shin kin taɓa samun wani ƙalubale a gida yayin da kika fara rubutu? Wanne goyon baya kika samu daga wajen iyaye ko makusantanki?

Gaskiya a baya na samu ƙalubale sosai musamman ta wajen maigidana, amma kuma a gida na samu goyon baya daga wajen iyayena.

Da wanne lokaci kika fi jin daɗin yin rubutu?

Da daddare, ko da safe, saboda na fi samun natsuwa wajen yin rubutu. Sannan na fi jin nishaɗin rubutu  idan ina cikin farinciki. 

Cikin littattafan da ki ka rubuta wanne ne ya fi jawo miki mabiya?

‘Silar Fyaɗe’, ‘Abin Cikin ƙwai’, ‘Doctor Nawwara’, ‘Auren Dole’, da 

‘ɗinyar Makaho’. 

Yaya mu’amalarki take da masu karatun littattafanki? Shin shawarwarin su ko ra’ayinsu yana iya tasiri wajen sauya akalar rubutunki?

Ina da mu’amala mai kyau da mabiyana, duk da wani lokacin akan samu kuskuren fahimta da wasu makaranta, amma Alhamdulillahi akasarin su muna da kyakkyawar mu’amala. Sai dai gaskiya ba na canja ra’ayi akan abin da zan rubuta, saboda mafi yawancinsu duk labarin gaske ne.

Mene ne ra’ayinki game da ɗora littattafanki a manhajojin sayar da littattafai, a maimakon fitarwa ta WhatsApp? 

Ina ɗora littattafaina sosai akan manhajojin sayar da littattafai, saboda gaskiya ta nan ma ana ƙara sanin rubutun mutum. Sannan ana ƙaruwa da fasaharka ta nan ma.

Me ki ke fara tunani kafin ki rubuta labari?

Abin da nake fara la’akari da shi shi ne, jigo, ma’ana ginshiƙin labari. Da zarar na fahimci me labarin zai ƙunsa da sunan da ya kamata na sa masa, shi kenan sai na duƙufa rubutu. 

Wanne irin salon rubutu ne ya fi birgeki, almara, soyayya, tarihi ko zamantakewa?

Gaskiya salon da ya fi burgeni shi ne salon zamantakewa. Sai kuma salon labarin abin dariya.

Wanne abu ne ya fi birgeki a mu’amala da sauran marubuta, kuma me kike ganin yake buƙatar a samu gyara a kai?

Gaskiya marubuta suna da haɗinkai sosai, amma abin da ya kamata a gyara shi ne rubutun batsa. A gaskiya rubutun batsa na sanyawa ana mana wani irin kallo na marasa tarbiyya.

Shin kin taɓa shiga wata gasar marubuta? Wacce shekara kuma wanne labari?

E, na taɓa shiga. Akwai Gasar ‘Taskar Nabilancy’, wacce na zo ta uku a shekarar 2021. Sannan akwai Gasar Hazaƙa Writers Association da aka yi a shekarar 2023, ita ma na samu nasara a ciki. Sai kuma Gasar Zauren Marubuta da aka yi cikin wannan shekarar ta 2024, ita ma na samu nasarar zama ta biyu da labarina mai taken ‘Silar Bincike’. 

Waɗanne abubuwan alheri ki ka samu ta dalilin rubutu? Kuma ko akwai abin ɓacin rai da kika taɓa fuskanta?

Gaskiya na samu alheri sosai, kuma ina ma kan samu, Alhamdulillahi. Kuma gaskiya ne ana fuskantar ɓacinrai sosai, musamman daga wajen mabiya, wani lokacin ba sa yi wa marubuci uzuri. Idan na fara labari kullum sai na ɗora cigaban labarin, wato na yi musu update, alhalin yau da kullum sai Allah. Amma da zarar watarana an samu tsaiko sai ka yi ta jin maganganu iri-iri. Wasu masu karatun ba su da haƙurin jira, musamman idan suna ganin sun biya kuɗin littafin ne. 

Shin kina samun damar karanta littafin wasu marubutan? Wanne littafin kike karantawa yanzu?

E, ina karanta littattafan marubuta da dama, kuma yanzu haka ma ina kan karanta littafin ‘Rana ɗaya’ ne wanda ƙawata Amira Adam ta rubuta. 

Shin kina karanta littafin da wani namiji ya rubuta? Mene ne dalili?

E, ina karanta littattafan marubuta maza. Dalili kuwa shi ne, su ma dai marubuta ne kuma suna da fasaharsu.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke? Kuma wanne abin cigaba ta taɓa yi miki, don inganta rubutunki?

Ni mamba ce a ƙungiyar marubuta ta Arewa Writers Association. Sannan kuma ƙungiyarmu tana bani ƙwarin gwiwa sosai, musamman wajen bita da shawarwari na yadda zan inganta rubutuna, da mu’amalata da sauran marubuta, har ma da fannin zamantakewata da jama’a.

Wanne muhimmin saƙo kike da shi ga marubuta?

Muhimmin saƙona shi ne, mu ƙara haƙuri da juna. Nasan marubuta muna karɓar gyara musamman idan aka yi mana gyara ko shawara ta yadda ya dace. Nasiha ta a nan ita ce, don Allah mu riƙa haƙuri da masu ba mu shawarwari ko gyara akan rubuce-rubucenmu. Domin Bahaushe ya ce, gyara kayanka ba ya taɓa zama sauke mu raba. Kuma gyara ba ya taɓa zama ɓarna. 

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a rayuwarki? 

Babban burina shi ne na zama uwa tagari.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki? 

Dan hakin da ka raina…

Alhamdulillahi. Na gode. 

Masha Allah. Ni ma na gode ƙwarai da gaske.