Shekara biyu ina neman mutumin da ke damfarar mutane da suna na – Sheikh Abdallah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sheikh Abdallah Gadon ƙaya ya bayyana cewa shi ma kusan shekaru biyu ya kwashe yana neman Aminu Abdullahi, mutumin da ‘yan sanda suka kama shi bisa zargin damfarar ‘yan kasuwa a jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Laraba ta sanar da cafke Abdullahi, mai shekaru 50 da haihuwa bisa zargin amfani da sunan Sheikh Abdallah ya cuci al’umma.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama shi ne bisa ƙorafe-ƙorafen da wajen mutane 20 suka kawo cewa ya sayi kayansu amma bai tura musu kuɗin ta banki ba, inda ya ke ce musu zai aiko kuɗin an jima kuma shi ƙanin Sheikh Abdallah ne, don haka kar su damu.

Sai dai shi ma Sheikh Abdallah, a hirar da ya yi da Freedom Radio ya nuna takaicin yadda mutumin ke amfani da sunansa ya na damfarar al’umma.

A cewar Sheikh Abdallah, mutane da dama sun zo wajensa don bin bahasin kuɗaɗensu na kayan da su ka ce mutumin ya saya da sunansa, inda malamin ya ƙara da cewa shi ba ya cim bashi kuma ba wani kaya da yanke siya bashi.

Sheikh Abdallah ya kuma yaba wa rundunar ‘yan sanda bisa kamo mutumin, inda ya kuma yi kira ga al’umma, musamman ‘yan kasuwa da su kiyaye kuma su daina yadda ana amfani da sunansa wajen damfararsu.