Shekarar 2024 ce mafi tsanani ga ma’aikatan Nijeriya, inji NLC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta bayyana shekarar 2024 a matsayin shekarar da ma’aikata suka fi fuskantar ƙalubale a ƙasar.

Joe Ajaero, Shugaban NLC, ya bayyana haka a ranar Litinin a Abuja, a wajen wani taron Makarantar Harmattan na 2024.

Taron na Makarantar Harmattan, taro ne na shekara-shekara da NLC ke shiryawa, wanda ke aiki a matsayin shirin ilimantar da ma’aikata da sauran tsare-tsare.

Ya ce, shekarar 2024 ga ma’aikata a ƙasar nan ta zo da tsananin wahala.

Ajaero ya umarci ma’aikatan da ke shiga makarantar harmattan da su himmatu a cikin horon wanda a cewarsa, an yi niyya ne don shirya ma’aikata don haɗin gwiwa da tattaunawa don sabuwar kwangilar zamantakewa.

A cewarsa, makarantar harmattan ta bana ta ba da damar rarraba duk abubuwan da suka faru ga NLC a cikin wannan shekara, tantance yanayin su, da kuma ƙaddamar da matakan da za a iya ɗauka don ƙara ƙarfafa kanmu da ingantawa.

“Mun yi imanin cewa a cikin waɗancan al’amuran, mun fito da ƙarfi, da juriya da matsayi mafi kyau don isar da tsammanin ma’aikata da mutanen Nijeriya,” in ji shi.