Shettima ya ƙaddamar da taraktoci 375 da Hukumar NASENI ta ƙawata a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da motocin tarakta guda 375 na Gwamnatin Jihar Borno waɗanda Hukumar Kula da kayayyakin Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa (NASENI) a ƙarƙashin Ofishin aikin kula da kadarorin ƙasa, gyara su da raba su ta ƙawata.

A ranar Lahadi aka gudanar da taron a ofishin hukumar kula da kayan aikin noma (BOSAMA) ta jihar a Maiduguri.

Shettima ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da jagoranci a jihar.

Haka kuma ya jinjina wa NASENI kan aiki tuƙuru da ta ke yi wajen haɓaka harkar noma a zamanance da shirye-shiryen da ta ke aiwatarwa.

A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya bayyana farin cikinsa ga yadda Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ke shiga ciki ayyukan ci-gaba musamman wajen bunƙasa harkar noma a Borno a lokacin da ya ke gwamna a jihar daga shekarar 2011 zuwa 2023 da kuma a yanzu.

Shettima ya kuma ƙaddamar da kayan aikin noma guda 351 da gwamnatin jihar ta sayo waɗanda za su taimaka wajen sauƙaƙe harkokin noma ga al’ummaa jihar.

By Babaji