Janar Buratai ya tsallake rijiya da baya harin ƴan ta’adda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu mayaƙan Boko Haram suka kai wa tsohon shugaban sojojin hari, ranar Juma’a.

Lamarin ya tada ƙura duba da yadda ya taimaka wa ta’azzara da ayyukan ta’addanci ke yi a shiyyar Arewa ta Gabas.

Sanata Ali Ndume ya bayyana hakan a yayin hira da gidan telebijin na Channels a yammacin ranar Lahadi.

Ya ce, an farmaki Buratai da wasu sojoji ne a kusa da wani babban sansanin sojoji.

Duk da cewa ba samu cikakken bayani kan al’amarin ba, Sanatan ya ce an yi musayar wuta a tsakanin maharan da sojojin da ke rakiyar tsohon shugaban sojojin.

Ya kuma ce, maharan sun yi nasarar lalata da dama daga cikin kadadorin sojojin a lokacin da suka kai harin da wasu muggan makamai.

Sanata Ndume ya ƙara da cewa, mayaƙan suna yawo a sake tare da sace kayan yaƙi na sojoji, lamarin da ke ƙara faɗaɗa ayyukan ta’addanci a jihar da dama shiyyarbaki ɗaya.

By Babaji