
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shatima ya ƙaddamar da tsarin ci-gaba mai dogo zango a shiyyar Kudu maso Gabas, wanda ake sa ran zai kammala nan da shekaru 25 masu zuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa Shettima ya ƙaddamar da tsarin ne a taron ƙungiyar masu ruwa da tsaki na shiyyar, wanda aka gudanar a Inugu, inda ya sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar da Kamfanin Zuba jari na Kudu maso Gabas domin samar da kuɗin tallafa wa ci-gaban yankin.
A cewarsa, sabon tsarin zuba jarin ya ƙunshi samun tallafi daga ƙasashen waje, manyan kasuwanni da cibiyoyin kuɗi na ci-gaba domin tallafa wa tsarin dogon zangon da kuma zuba ayyukan ci-gaba a sassan shiyyar.
Shettima ya bayyana ƙungiyar a matsayin wadda ta taimaka wajen kawo ƙarshen shugabanci masu gajerun zango, yana mai cewa hangen shekarar 2050 a matsayin abin hari ga ci-gaban yankin shi ne mafita ga gobensa.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa, kamfanin zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Raya Shiyyar Kudu maso Gabas (SEDC) domin maye gurbin ababen more rayuwa da aka rasa tun bayan yaƙin basasa, bunƙasa ababen da ake samarwa da faɗaɗa matakan gogayya na dogo zango.
Kazalika, Shettima ya jaddada ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ciyar da shiyyoyin Nijeriya gaba, inda ya ce hukumar SEDC tana aiki ne na samar da sauyin ci-gaba a sassan jihohin yankin a madadin taƙaice ayyukanta a iya sashin gudanarwa.
Wannan taro ya kasance muhimmin al’amari wajen fita daga tsarin mulkin ƙaramin lokaci zuwa tsarin tsare-tsare na ci-gaba na shekaru da dama.
