Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Bayanin zaman majalisar zartaswa ta Jihar Katsina na uku a wannan shekara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da wannan.
Haka kuma majalisar ta aminta da samar da na’urar wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar PV)mai ƙarfin 2MWH donin amfani da su a wasu ma’aikatu wanda hakan zai rage kuɗaɗen da ake kashewa wajan man fetur,da inganta ɗorewar samar da wutar lantarki a muhimman gine ginen gwamnati.
Kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya ce a bayanin da ya faɗawa manema labarai, majalisar ta amince da tsarin shirin da zai jagoranta tare da kula da ayyukan ƙungiyoyin sa kai na ƙasa da ƙasa da na cikin gida masu zaman kansu (INGOs/NGOs) a Jihar Katsina.
Tsarin inji kwamishinan zai kula da tabbatar da ɗaukar ma’aikata bisa ƙa’ida tare da bai wa ‘yan asalin jihar da mazauna jihar masu cancanta fifiko, tabbatar da gaskiya da sa ido kan ayyukan, ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumar kula da ci gaban Jihar Katsina (KTDMB), samar da ayyukan yi ga matasa da gina ƙwarewa ga yan cikin gida, da kuma ƙarfafa amincewa da fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da abokan hulɗar ci gaba.
Haka kuma ta amince da tabbatar da tsarin samar da horo ga ma’aikatan da su ka fi buƙata kuma suka cancanta. Ya ce a baya, yawancin bita da horaswa ana saka iya waɗanda ake so ko da ba su buƙata wanda hakan yana sawa a yi asarar kuɗin gwamnati wajen horaswar saboda ritaya ko wani abu mai kama da haka. “Amma yanzu wannan sabon tsarin zai tabbatar da cewa duk wanda za a horas jiha za ta amfaneshi,”Inji Dr Bala Zango
Harwala yau majalisar ta amince da aiwatar da shawarwarin da aka bayar lokacin babban taron tattaunawa kan tsaro da mulki da mai girma gwamna Raɗɗa ya kira.
“Waɗannan shawarwari za su zama taswira ta inganta zaman zaman lafiya a Jihar Katsina,”kwamishinan ya ce.
