Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), ta bayyana cewa yawan motocin da aka shigo da su ta tashoshin jiragen ruwa na ƙasar ya ƙaru da kashi 67 cikin ɗari a farkon shekarar 2026 idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025.
Bayanan da ke cikin rahoton nazarin ayyukan hukumar na watanni ukun farko na 2026 sun nuna cewa an sarrafa motoci 58,870 a tashoshin jiragen ruwa daban-daban na ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2026, sabanin motoci 35,262 da aka samu a irin wannan lokaci a bara.
Rahoton ya kuma nuna cewa harkokin sufuri ta ruwa a Nijeriya sun samu bunƙasa sosai a wannan lokaci, inda jimillar ƙarfin lodin manyan jiragen ruwa masu zirga-zirga a tekuna ta ƙaru da kashi 19.5 cikin ɗari zuwa ton miliyan 46.75.
Wannan ci gaba na nuni da yadda ake ƙara amfani da manyan jiragen ruwa masu ɗaukar kaya masu yawa a tashoshin Nijeriya, yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara aiwatar da gyare-gyare domin ƙarfafa matsayin ƙasar a matsayin cibiyar kasuwanci a yankin Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar Kasuwancin Nahiyar Afirka, wato African Continental Free Trade Area.
A cewar NPA, ƙaruwar tan ɗin jiragen ruwa na nuna ingantuwar yadda ake jigilar kaya tare da ƙara amincewar kamfanonin sufurin ruwa na ƙasa da ƙasa da tsarin tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya.
Hukumar ta danganta wannan ci gaba da ƙara muhimmancin Tashar Ruwa Mai Zurfi ta Lekki, Lekki Deep Sea Port, da kuma bunƙasar harkokin kasuwanci, tana mai cewa ana komawa amfani da manyan jiragen ruwa masu inganci a harkokin sufuri.
Rahoton ya ƙara da cewa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na sabunta kayayyakin more rayuwa a tashoshin ruwa, inganta ayyukan sauke kaya da kuma jawo ƙarin harkokin kasuwanci daga yankin Afirka ƙarƙashin tsarin AfCFTA na taimakawa wajen wannan gagarumin ci gaba.
Jimillar kayan da aka sarrafa a tashoshin ruwa, ban da man fetur, ta ƙaru da kashi 11.6 cikin ɗari daga tan miliyan 29.02 a rubu’in farko na 2025 zuwa tan miliyan 32.38 a rubu’in farko na 2026.
Hukumar ta danganta wannan ƙaruwa da bunƙasar kasuwanci, ingantuwar harkokin shigo da kaya da fitarwa, da kuma ƙaruwa a buƙatar ayyukan tashoshin ruwa.
Fitar da kaya zuwa ƙasashen waje ta samu ɗaya daga cikin manyan nasarori, inda ta ƙaru da kashi 23.7 cikin ɗari zuwa tan miliyan 14.13. Hukumar ta ce hakan na nuna ƙarfafa ƙarfin fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa kasuwannin duniya da kuma ƙarin shiga cikin tsarin samar da kayayyaki na yanki da na duniya.
Haka kuma, yawan kwantena masu kaya da aka fitar zuwa ƙasashen waje ya ƙaru da kashi 67.6 cikin ɗari daga TEUs 61,332 a rubu’in farko na 2025 zuwa TEUs 102,803 a makamancin lokacin 2026, sakamakon ingantuwar tsarin fitar da kaya da ayyukan tashoshin ruwa.
Ayyukan jigilar kwantena daga wata ƙasa zuwa wata ta tashoshin Nijeriya ma sun ƙaru da kashi 83.1 cikin ɗari, lamarin da ya ƙara ƙarfafa matsayin Nijeriya a harkokin kasuwancin ruwa da dabarun sufuri a yankin.
NPA ta bayyana cewa wannan ci gaba na nuna yadda masana’antar harkokin ruwa ta ƙasar ke ƙara zama cibiyar kasuwanci mai ƙarfi da kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da haɗa Nijeriya da kasuwannin yankin.
Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Legas, Manajan Daraktan NPA, Abubakar Dantsoho, ya jaddada buƙatar tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya su zama masu gogayya a sabon tsarin kasuwancin Afirka.
Ya ce ƙwarewa, sabbin fasahohi, saurin aiki da kuma inganci ne za su tantance ƙasashen da za su mamaye harkokin jigilar kaya ƙarƙashin yarjejeniyar kasuwancin nahiyar.
Dantsoho ya ƙara da cewa tsarin tashoshin ruwa na Nijeriya na da damar zama ginshiƙi wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa idan aka yi amfani da albarkatun ruwa yadda ya kamata.
