Shin ko kun san amfani da bayi mai datti ba ya haifar da ciwon sanyi na mata?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barka da yau, barkanmu da sake ganin wani sati lafiya.

Darasin mu na yau dai zai ƙaryata daɗaɗɗiyar magana da muka sani kuma muka yarda da ita lokaci mai tsayi, ba kuwa don komai muka aminta da ita ba face ire-iren mutane da ke gabatar da ita gare mu, wato waɗanda muke yi wa kallon masana.

Mun jima muna kiran cutar sanyi na mata da suna ‘toilet infection’ ma’ana cutar da ake samu a bayi mai datti. Mun jima da ji kuma mun amince da hakan, wannan ya sa da yawa mata ke taka-tsan-tsan da inda za su yi tsuguni, da kuma ƙoƙarin tsaftace ban ɗakinsu akai-akai. 

Yin hakan abu ne mai matuƙar muhimmanci, kuma bijirewa hakan na haifar da cuta, saidai ba ta sanyi ba kamar yadda muka zata.

Bayi mai datti ba shi da alhakin haifar da ciwon sanyi na mata, duk da cewa zai iya ɗaukar alhakin wasu ababen masu cutarwa na daban.

Asalin kalmar ‘toilet infection’ ba haifaffiyar kalmar kimiyar lafiya ba ce. Sauƙaƙƙar kalma ce wadda jama’a ke amfani da ita don bayanin alamonin cutar ‘ɓulɓoɓaginitis’ kamar ƙaiƙayi, zafi a farjin mace, fitar ruwa masu wari, da sauransu.

Saidai ba a iya amfani da kalmar aka tsaya ba, ana amfani da kalmar ta ‘toilet infection’ saboda tunanin wannan cutar na samuwa ne ta hanyar amfani da bayi mai datti.

Vulvovaginitis na nufin hausin (inflammation), vulva da vagina. A sa’in da ɓagina kawai ta kamu ana kiran cutar ɓaginitis, sa’in da ɓulɓa kawai ta taɓu ana kiran shi ɓulɓitis. Amma mafi akasari ana kiran cutar kawai ɓaginitis. 

Ita wannan cuta da masana lafiya suka kira da ɓaginitis cuta ce da ta zama ruwan dare a tsakanin mata, domin kaso biyu bisa uku na mata suna samun ciwon ko sun samu, musanman ma a lokacin ganiyar balagarsu, wato daga sha shida zuwa arba’in. 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi