



Daga BELLO A BABAJI
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaddamar da aikin raba tallafi ga ƙananan makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin inganta mata da ba su ilimi (AGILE) a jihar.
A ranar Laraba ne gwamanan ya miƙa takardun bada ayyukan ga ƴan kwangilar gyarana makarantu.
Cikin wata sanarwa da kakakin gwamanan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce an shirya aikin ne musamman don inganta hanyoyin samun karatu, cigaba da karatu da kuma biyan wani kaso a makarantun jihar.
Ya kuma ce, wannan shi ne zangon farko na shirin SIGS ƙarƙashin ayyukan AGILE.
A lokacin da ya ke magana, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa makarantu 322 aka zaɓa yayin gudanar da aikin wanda zai haɗiye N11,736,000,000.
Ya ce, wannan ɗaya ne daga cikin muhimman alƙawuran da suka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe wanda aciki akwai batun inganta harkar ilimi.
Gwamnan ya yi kira ga waɗanda aka bai wa ayyukan gyaran su tabbatar an kashe kowane ɓangare na kuɗin wajen yin aiki mai nagarta a makarantun.
Bugu da ƙari, Dauda Lawal ya yi kira ga tawagar masu kula da aikin da kwamitocim gudanarwa na makarantu (SBMCs) da kuma al’umma su kasance masu sanya ido kan gudanar ayyukan inda ba iya makarantun ba, har ma jihar baki ɗaya hakan zai inganta.
