

Daga BELLO A. BABAJI
Tsangayar Labarai ta Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria a jihar Kaduna ta samu sabon Darakta bayan da aka bai wa Sani Musa Daitu muƙamin.
Cikin wani saƙo da ya fitar, Musa Daitu ya ce “ina farin cikin sanar da ku cewa, Ni, Sani Musa Daitu, an naɗa Ni a matsayin Daraktan Labarai a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria.”
Ya ce, an ba shi muƙamin ne wanda zai riƙe na tsawon shekaru uku (2024-2027), ya na mai alƙawarin zai yi aiki tuƙuru wajen ganin an cimma manufofin ofishin.
Ya ƙara da cewa, zai bada gudunmawa da ƙwarewarsa wajen samar da nasarori da cigaba musamman kan salon yaɗa labarai a kwalejin.
Har’ilayau, ya miƙa godiyarsa ga Majalisar amintattu ta kwalejin kan damar da suka ba shi ta aikin wajen samar da cigaba a ɓangaren harkar ilimi a Nijeriya.
