Shin wane ne Marigayi Sheikh Ahmad Bamba?

Daga ABDUL HAQ

An haifi Sheikh Dakta Ahmad Bamba a shekarar 1940, sannan ya taso a garin Alabar A.E.B ko Nguwan Gonjawa, a Jihar Kumasi ta ƙasar Ghana.  Mahaifinsa shi ne, Muhammad Ibrahim Bamba iyayensa mata su ne, Hajia Khadijah (Mma Adizatu) and Hajia Fatima (Mma Hajia), su kuma sun kasance ‘ya’ya ne a wajen Mma Gyamata. Ita kuma Gyamata ta kasance ‘ya a wajen  shahararren malamin addini sannan dattijo na farko a unguwar Gonja ta jihar Kumasi. Wato Marigayi Mallam Sani. 

Ya fara ɗaukar darasin ilimin addini a wataniyya a ƙarƙashin sanannen Sufin nan, Alhaji Baba Al-Waiz. Wanda aka fi sani da  Babal-Waiz a Kantudu.  

Duk da haka kuma ya yi saukar karatunsa a ƙarƙashin koyarwar mahaifinsa a masallacin Kakan Kakansa wanda yake a garin Afia Kobi. Daga nan sai ya cigaba da zurfafa iliminsa a kan fannin hukunce-hukuncen shari’a (fiqihu). Inda ya fara da littafin Al – Ishmawiy wanda yake ɗauka a gaban Mallam Amadu Langonto. Daga nan kuma ya koma gaban babban Malamin da ya jaddada Sunnah a Kumasi, Sheikh Abdul Samad Habibullah. 

Abokan karatun Shehin sun haɗa da: Mallam Imrana Musah, tsohon limamin masallacin Ashanti. Sai tsohon halifan Wataniyya, da mai ci yanzu, Mallam Muntari. Sai sarkin limaman garin Dagomba, Alhaji Lawal na Baba Abbas wanda aka fi sani da Alhaji Nuhu Abbas. Sannan akwai Mallam Zakari Alhaji Nuhu na Kotokoli. Sannan Ustaz Umar, Sarkin limaman garin Yadiga da kuma irin su Mallam Muhammad Danraz da Mallam Dan Azumi, da sauransu. 

Yana da kyau a san cewa, amininsa  Mallam Muntari shi ne ya fara kai Dakta Bamba kuma ya ba shi shawara ya nemi ilimi a gaban Sheikh Abdul Samad bayan Shaihin ya yi masa ƙorafin nisan tafiyar dake tsakanin  Alabar birnin Accra (Oforikrom) inda Malaminsa Mallam Amadu yake da zama. A lokacin shi ma Mallam Muntari ya jima yana ɗaukar karatu a makarantar gaban  Sheikh Abdul Samad a dai-dai inda asibitin garin Manhyia yake a yanzu.

Mallam Muntari ya bayyana cewa, bayan neman ilimin da yake kuma, Dakta Ahmad Muhammad Bamba ya koyi ɗinkin kaya daga Mallam Awudu, wanda shi ma abokin karatun nasu ne. Sannan bugu da ƙari, ya yi sana’ar kiwon shanu wanda ya koya a wajen Mallam Muntari wanda shi kuma mahaifinsa sana’arsa ita ce sayar da shanu a mayankar garin Kumasi. 

Duk da kasancewar ya tsunduma cikin sana’o’i daban-daban, wannan bai saka shi yin wasarere da harkar neman iliminsa ba, har sai da ya tattara tarin ilimi mai yawa daga wajen Sheikh Abdul Samad da wajen wasu Malamai Misrawa waɗanda gwamnatinsu ta ɗauki nauyinsu su zo garin Kumasi domin su buɗe wata makaranta mai suna Markaz Al-Sharif, inda za a dinga koyarwa kyauta. 

Sheikh Ahmad Bamba da aminninsa  Mallam Muntari ba su yi wata-wata ba suka tsunduma kansu a makarantar. Bayan an ɗan samu lokaci ana koyarwar, sai malamin nasu ya lura da irin ƙoƙarin da Sheikh Ahmad Bamba yake da shi na kaifin haddar riƙe karatu. Wannan ya sa aka ba shi damar zuwa ƙasar Misira domin ya ƙaro ilimi. Amma sai dai bayan wata guda sai ya bayyana muradinsa na son zuwa ya karanci kimiyyar Hadisai a babbar jami’ar Madina.  A inda ya samu digiri a kan kimiyyar hadisai (koyarwa da ayyukan Annabi S.) Daga nan kuma ya je jami’ar Bayero ta Kano ya yi digirinsa na biyu da na uku. 

Sheikh Dakta Ahmad Bamba ya kasance ɗaya daga cikin manyan ɗalibai ga babban malamin addinin Islamar nan na Jami’ar musulunci ta Madinah, Sheikh Hamad Bin Muhammad Al – Ansari. Sannan ya bar tarihi mai girma a lokacin rayuwarsa a matsayin ɗalibin jami’ar. 

Jami’ar Musulunci ta Madinah da kuma Jami’ar Bayero ta Kano dukkansu sun ayyana Dakta Ahmad Bamba a matsayin babban masanin hadisai. Wannan shi ne mafarin zaman shehin a Jihar Kano a Nijeriya. Inda ya zauna a matsayin Malamin jami’a kuma Malamin addini tun a lokacin shekarun Alif ɗari tara da tamanin har i zuwa lokacin rasuwarsa. 

Sheikh Dakta Ahmad tsohon malamin jami’a ne da ya koyar a Jami’ar Bayaro ta Kano. ya koyar a tsangayar Ilimin Islama sannan ya cigaba da karantar da mutane ta hanyar wa’azi da littatafan hadisai a masallacin Jami’ar daga baya kuma ya koma masallacin ƙashin kansa mai suna Darul Hadith da ke Kano, a Unguwar Tudun Yola. Inda yake limami kuma shugaba. 

Sheikh Dakta Ahmad Bamba ya rasu ya bar matan aure guda 3 da ‘ya’ya 30 da kuma jikoki da dama. Matarsa ta fari ita ce, Hajia Rubama, ‘ya ce ga Alhaji Kassimu na Aboabo. 

A cewar ‘yan uwan Dakta Ahmad Bamba, Alhaji Isshaku da Alhaji Salu Bamba, Alhaji Kassimu ya damqa amanar Rubama a hannun Hajia Fatima (Mahaifiyar Dakta Ahmad Bamba). Bayan ta karɓi amanar ne, sai ta ce: “Ina fatan za ta kasance mata ga Ahmad Bamba”. Alhamdulillahi kuma sai Allah ya amsa addu’arta. 

Sheikh Dakta Ahmad Bamba ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen bautar Allah da hidima ga mutane. A cewar Dakta Umar Sani Rjiyar Lemo, idan ka ɗebe ƙoƙarin Sheikh Mahmoud Gumi, Dakta Ahmad Bamba shi ne masani  hadisi na farko wanda ya kammala cikakken sharhi a kan dukkan littatafan sahihan hadisai guda shida mai suna Kutub al-Sittah a Larabce su ne:
Sahih al-Bukhari;
Sahih Muslim;
Sunan Abu Dawood;
Sunan al-Tirmidhi;
Sunan al-Nasa’i/al-Mujtaba;
Sunan ibn Majah.

Sannan ya yi karatunsa na boko a wani gari mai suna Roman Hills a Kumasi. Inda ya fito da sakamako mai kyau. Haka Sheikh Adam Baba da Alhaji Abdulai Ayayi, an ce abokan karatunsa ne. 

Da ya ke tsokaci a kan mu’amalar Marigayin, Mallam Muntari, ya bayyana Sheikh Dakta Ahmad Bamba a matsayin mutum mai ƙan-ƙan da kai kuma abin girmamawa. Shi ya sa ma a cewar sa ya zama abin so ga kowa har ma ga mahaifinsa, Alhaji Iddi Maishanu. An haife shi ne a babban gida, inda ya ke da ƙanne da yayye masu yawa. 

Yayyensa da qanne maza sun haɗa da Mallam Adam Bamba Sufi, Sheikh Aminu Bamba, Alhaji Abdul Aziz Bamba, Mallam Saidu Bamba, Alhaji Isshak, Alhaji Salu Bamba, Alhaji Mahmoud, Alhaji Farouk, Alhaji Wasiu, Sheikh Suleman Bamba, Alhaji Adam, Alhaji Usama, Alhaji Sadiku, Alhaji Hashiru Hamburg, da sauransu. 

Yayye da ƙannensa mata su ne Hajia Awuraba, Hajia Kande, Hajia Baida, Mma Muhamdiyya, Hajia Iya, Hajiya Aunty Bamba, Hajiya Zulai, Hajia Safura Bamba, Hajiya Amatu Khalid, Hajia Barkisu, Hajiya Abbatu da sauransu. 

“Ahmadu Bamba, Allah ya yi maka jin ƙai,” waɗannan su ne kalaman ‘yar uwarsa,  Hajiya Awuraba.

Malam Abdul Haq jika ne ga Marigayi Sheikh Ahmad Bamba. Amina Yusuf Ali ce ta fassara wa Jaridar Blueprint Manhaja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *