Na ba ka kwanaki uku mu ajiye muƙamanmu – Mataimakin gwamnan Zamfara ga Gwamna Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mataimkin Gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Mohammed Gusau ya ce a shirye yake ya bada takardar barin aikin shi na matsayin mataimakin gwamnan Jihar Zamfara muddin shi uban tafiyar, Gwamna Matawalle zai rubuta tashi takardar ta barin muƙamin shi na gwamna kamar yadda ya yi iƙirarin  yi a wata hira da ya yi da ‘yan jaridu a gidan gwamnati a satin da ya wuce. 

A cikin hirar, gwamnan ya yi rantsuwa da Allah cewa da ba don sanin da ya yi cewa ɗan Ali Gusau ne zai hau kujerar gwamna ba bayan shi Matawallen ya sauka, da tuni ya sauka daga kujerar ta gwamnan, inji shi.

Da yake mayar wa gwamnan da martani, mai magana da yawun mataimakin gwamnan ya yi Allah wadai da wannan magana wadda ya kira ta tamkar ‘soki burutsu ne kawai’. Ya zargi Matawalle da laifin wasa da hankalin mutannen jihar. 

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan ya ƙara jaddada cewa a shirye mataimakin gwamnan yake ya sa takardar barin aikin shi a duk ranar da shi maigirma gwamnan zai sa tashi. 

Ya ƙara da cewa wannan ƙuduri da matamaikin gwamnan ya yi na barin aiki tare da shi da Gwamna Matawalle yana daga cikin sadaurkarwa na ganin an ceto Jihar Zamfara daga mummunan halin da ta samu kanta. 

Ya kuma ƙara da ba Gwamna Matawalle shawara da ya mayar da hankali wajen shirin yadda zai tafiyar da rayuwar shi bayan ya sauka daga mulki, wanda ga dukkan alamu ya kusa, a cewarsa.