Yadda Nijeriya ta lallasa Masar a gasar AFCON

Daga WAKILINMU

Kelechi Iheanacho na Super Eagles ya cirewa Nijeriya kitse a wuta a karawarta da Masar ranar talata bayan ƙwallonsa da ta bai wa ƙasar ta yammacin Afrika nasara a wasanta na farko ƙarƙashin gasar cin kofin Afrika.

Shahararren ɗan wasan gaba na Liverpool Salah bai taɓuka abin kirki ba, sakamakon yadda zaratan ’yan wasan Nijeriya suka riƙe shi tsawon mintuna 90 da aka yi a wasan.

Babban wasa na biyu da kowa ke jiran gani a gasar cin kofin Afrika na shekarar 2021 tsakanin Nijeriya da Misra, ya zo ƙarshen inda Nijeriya ta yiwa Misra da shahararren ɗan wasanta Mohamed Salah ci ɗaya mai ban haushi.

Bayan wasan Ghana da Morocco a ranar Litinin da ita ma Ghana ta sha ci ɗaya da nema, wasan da aka kwatanta da karan batta da ake gani kowane ɓangare na iya ɗaukar kofin, sakamakon wasan Nijeriya ce ta yi shirin ɗaukar kofin gasar Afrika ta bana.

Shahararren ɗan wasan gaba na Liverpool Salah bai taɓuka abin kirki, sakamakon yadda zaratan ’yan wasan Nijeriya suka masa riƙe shi tsawon mintuna 90 da aka yi wasan.

Ƙwallon da Kelechi Iheanacho ya zura a zagayen farkon wasan ya bai wa Nijeriya damar tattara maki uku na wasan.

Ana sa ran ƙungiyoyin wasan ƙasashen biyu za su yi fice daga rukunin D zuwa matsayi na gaba duk da sakamakon wasan na yau, amma nasarar da Super Eagles ya gayara mata hanyar isa ga zagayen da ƙasashe 16 za su fafata kana ya ba ta ƙwarin gwiwa a wannan gasa, yayin da ita Misra ta ke cikin damuwa a lokacin da ta ke Shirin yin sauran wasanninta da Guinea-Bissau da Sudan.

Salah a tsakin ‘yan wasan Nijeriya

Moses Simon na ɓangaren Nijeriya, shi ne ya fi taka leda a wasan, duba da irin rawar gani da ya taka a gefen filin wasan.

Yanzu Nijeriya za ta kara ne da Sudan a wasanta na gaba wanda za a yi a ranar Asabar.

Ita kuwa Masar za ta kara ne Guinea Bissau a ranar ta Asabar duka a rukuninsu na D.