Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kuma Shugaban Kwamitin Aiwatar Da Garambawul Na Kiwon Dabbobi, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa shirin Shugaban ƙasa na ɓangaren kiwo zai samar ayyukan yi miliyan biyar nan da shekarar 2030.
Jega ya kuna yi gargaɗi cewa Nijeriya na iya fuskantar kasadar ƙarancin sinadarin gina jiki ga yara idan ba a aiwatar da tsarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi na sake fasalin kiwon dabbobi ba.
Ya kuma bayyana cewa, a ƙoƙarin da ake na rufe giɓin furotin, a halin yanzu Nijeriya na kashe maƙudan kuɗaɗe har Naira Biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da kayayyakin kiwo, galibin madara, waɗanda ba su da amfani.
Jega, ya ce: “Ya zuwa shekarar 2030, tare da aiwatar da ayyukan sake fasalin kiwo na Shugaba Tinubu, Nijeriya za ta samar wa aƙalla mutane miliyan biyad ayyukan yi da suka haɗa ɓangaren aikin nama, kiwo, aikin fata da dai sauran su musamman ga matasa da mata a yankunan karkara.”
Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Saliu Mustapha, ya bayar da shawarar cewa a ware kashi 6-7 na kasafin kuɗin Nijeriya na shekara domin harkar noma don samar da ayyukan yi a ƙasar.
Duo ya yi magana a ranar Litinin a Ilorin, jihar Kwara, a taron shekara-shekara na Jami’ar Ilorin, don girmama ɗan majalisar.
Taken laccar ita ce “Tsarin Tattalin Arzikin Kiwo a Nijeriya: ƙalubale da Alfanu.”
Jega, a cikin takardarsa, ya ce: “Yin hasashen da aka yi ya nuna cewa nan da shekara ta 2050, al’ummar Nijeriya za su kai kusan miliyan 400, wanda hakan zai sanya ta zama ƙasa ta uku mafi yawan al’umma a duniya.
“Wazannan alƙalumman ba zato ba ne, kararrawa ce. Idan ba tare da ganganci, shiri da kuma zuba jari na dogon lokaci a tsarin kiwon dabbobi ba, Nujeriya na fuskantar kasadar fuskantar ƙarancin furotin, ƙƙra ƙarancin abinci da kuma matsananciyar matsin rayuwa a yankunan karkara.
“Ba za a iya cimma wannan buƙatu da aka yi niyya ba ta hanyar inertia na kasuwanci-kamar yadda aka saba. Maimakon haka, yana kira da a sake tunani game da gine-ginen sassan – wanda aka kafa a cikin ci gaba mai ɗorewa, samar da yanayi mai kyau da ci gaba.”
A nasa jawabin, Sanata Mustapha, wanda ya sanar da bayar da gudunmuwar kuɗi naira miliyan 10 ga tsangayar ilimin zamantakewa, ya buƙaci mahalarta taron da su duba ciki su yi la’akari da ɗaukar sana’ar kiwo a matsayin hanyar rayuwarsu.
