Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Laifukan zamba na yanar gizo na zama ɗaya daga cikin manyan barazanar tsaro a Afirka, tare da sama da kashi 30 na duk laifukan da aka ruwaito a Yammacin Afirka da Gabashin Afirka yanzu su na da alaƙa da ayyukan Intanet, a cewar sabon rahoton Hukumar ‘Yan Sanda ta ƙasa da ƙasa (INTERPOL) sahen Afirka na 2025 da aka fitar.
Rahoton, wanda ya zayyano bayanai daga ƙasashen Afirka da masu haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, ya yi nuni da cewa, kashi biyu bisa uku na ƙasashen da a ka gudanar da bincike a kansu, sun bayyana laifukan ta yanar gizo a matsayin babbar barazana.
Rahoton ya yi nuni da yadda ake samun ƙaruwar masu zamba ta yanar gizo, musamman masu satar bayanan sirri, inda wasu ƙasashen Afirka suka fuskanci sama da 3,000 na yunƙurin zamba a cikin shekarar da ta gabata. Kaspersky, ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar kamfanoni masu zaman kansu na INTERPOL, ya ba da gudunmawar bayanan da ke nuna tsananin wannan yanayin.
Sauran manyan barazanar yanar gizo sun haɗa da kutsa kai a Imel na kasuwanci (BEC), musamman a Nijeriya, Kenya, Afirka ta Kudu, da Masar.
Afirka ta Kudu ta samu kutse 17,849 a cikin 2024, Masar ta biyo baya da 12,281, Nijeriya da Kenya sun sami 3,459 da 3,030.
Waɗannan al’amura sun haɗa da kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa, kamar hukumar kula da tituna ta Kenya, da keta bayanan gwamnati, musamman kutse na Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya (NBS).
INTERPOL ta kuma lura da ƙaruwar kashi 60 a cikin lamurra na seɗtortion na fasahar zamani, inda masu laifi ke amfani da hotuna na gaske ko na AI don karɓar kuɗi a hannun mutane.
Daraktan Laifukan Intanet na INTERPOL Neal Jetton ya jaddada buƙatar gaggawar aiwatar da ayyukan ƙasa da ƙasa baki ɗaya.
Jetton ya yi gargaɗin cewa, “Wannan rahoton ya nuna yanayin barazanar da ke saurin canjawa.
Da yake nanata haka, Ambasada Jalel Chelba, muƙaddashin Darakta na AFRIPOL, ya jaddada illar aikata laifuka ta yanar gizo ga ci gaba.
“Tsaron yanar gizo ba kawai batun fasaha ba ne, yana da muhimmanci ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba mai ɗorewa.
