Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
A wani muhimmin mataki don inganta lafiyar jama’a, kamfanin Dexa Medica, masu ƙera magungunan rage ciwon jiki na Boska, sun ba da kulawar lafiya kyauta ga fiye da mutum 5,000 a jihohin Sakkwato, Adamawa, Bauchi, Kaduna, Ibadan, da Legas.
A lokacin shirin Pain-Free Day na kulawar da aka bayar ta kunshi duba lafiyar ido, gwajin hawan jini gwajin sukari tausa ga jiki, rabon gilasan ido kyauta, da magunguna masu muhimmanci.
Ana gudanar da shirin a kowane wata a jihohi daban-daban don tallafa wa lafiyar jama’a tare da nuna godiya ga masu amfani da kayansu.
Da yake jawabi a wajen taron, Afeez Olarewaju, jami’in TMP na Boska Group, ya jaddada cewa shirin ya fi mayar da hankali kan ‘yan kasuwa saboda galibinsu ba sa samun lokaci don kula da lafiyar su.
Shi ma da yake magana, Nurudeen Salawudeen ya bayyana cewa, “’Yan kasuwa muhimmin sashi ne na al’ummarmu kuma suna tallafa wa al’umomi. Wannan shiri wani hanya ce ta maidawa jama’a.
Ba kawai kan kula da ido muke mayar da hankali ba, har ma kan lafiyar jiki gaba ɗaya. Burinmu shi ne tallafa wa mutum 10,000 a kowace al’umma da aka zaɓa.”
Likitan ido, Dokta Abubakar, ya yi nuni da muhimmancin duba lafiyar ido akai-akai, inda ya jaddada cututtuka kamar su glaukoma, sankarau, da presbyopia waɗanda sau da yawa ba a gano su da wuri.
“Muna raba gilasan karatu fiye da guda 200 don taimakawa waɗanda ke da wahalar karanta rubutu ƙanana saboda tsufa”
Haka kuma muna bincika cutar glaukoma kuma muna turawa cibiyoyin lafiya idan aka samu matsaloli masu tsanani.
Mutane da dama suna karɓar magunguna da kuma jinya kyauta don cututtukan ido,” in ji shi.
Jakadiyar Boska, Muizat, ta bayyana cewa cututtuka irin su hauhawar jini sun yawaita a tsakanin ‘yan kasuwa, kuma galibi ba a gano su a kan lokaci.
“Ta wannan shiri, muna wayar da kai game da lafiyar jiki da kuma ƙarfafa mutane su riƙa ziyartar likitoci tare da ba da magunguna kyauta,”
Suleiman, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, wanda ya nuna godiyarsa ga wannan ƙoƙari, yana mai roƙon sauran kamfanoni su yi koyi da wannan aiki.
“Sun yi babban aiki sosai. Allah ya albarkace su. Ya kamata sauran kamfanoni su yi koyi da wannan ƙoƙari don tallafa wa al’umma,” in ji shi.
Shirin Pain-Free Day na ci gaba da faɗaɗa ayyukansa, yana ba da kulawar lafiya mai muhimmanci ga al’ummomin da ba sa samun isasshen kulawa a Najeriya, ciki har da Legas, Adamawa, Kaduna, Ibadan, da Bauchi.
Boska Nigeria na taya dukkan Musulmai murnar Sallar layya (Eid-el Kabir).
