An yi kira ga matasan yankin Funtua su rungumi noma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman yayi wannan kira a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa yankin Funtua wajen noma ne tun kaka da kakanni kuma kusan duk al’ummar yankin manoma “domin haka matasan Funtua ba su da zaɓi illa su rungumi noma.

Haka kuma a cewar kwamred Suleiman yankin Funtua na ɗaya daga cikin yankin da suka fi ko ina noma a ƙasan.

Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan ɓullo da amfani da fasahar zamani da zai taimaka wa manoma wajen haɓaka noma a jihar.

Yayi kira ga manoman yankin da suyi amfani da wannan fasahar da gwamnati ta samar domin faɗaɗa harkokin noma da bunƙasa tattalin arzikin su.

Shugaban ƙungiyar ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta shirya wa manoma wannan sabon tsari na noman zamani da zai taimakawa manoma wajen bunƙasa tattalin arzikin su da jiha baki ɗaya.

Kwamred Suleiman ya jinjina wa gwamna Raɗɗa kan aiwatar da muhimman ayyuka na raya ƙasa cikin shekara biyu da hawa mulkin Jihar Katsina.

Wasu daga cikin ayyukan da ƙungiyar ta jinjina wa gwamna kuwa sun haɗa da gina, tare da gyara manyan hanyoyi,gina makarantu da ɗaukar malaman firamare da na sakandare aiki da kuma maida ƙananan asibitocin zuwa manya da gina wasu a faɗin jihar.

Wajen harkar tsaro kuwa shugaban ƙungiyar ya ce duk da gwamna na bakin ƙoƙarin sa sai dai”yakamata gwamnati da masu ruwa da tsaki kan tsaro su tashi tsaye wajen tunkarar ta’addanci a yankin da jiha baki ɗaya.

By ukarofi