Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Jihar Zamfara Hon. Aminu Sani Jaji ya sayo raguna 3000 domin rabawa ‘yan mazaɓarshi da magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Shugaban Kwamitin gudanarwar na Jaji, Aliyu Abubakar MC ya sanar da hakan a Gusau yau Lahadi.
Ya ce, ɗan majalisar ya kuma ware kuɗi Naira Miliyan300,000,000 domin rabawa waɗanda suka cancanta, marayu da marasa galihu a faɗin jihar a matsayin gudummawar bikin Sallah.
“An yi wannan karimcin ne domin a taimaka wa mabiya addinin muslunci, ‘yan jam’iyyar APC da kuma iyalai marasa galihu wajen gudanar da bukukuwan sallah na bana cikin farin ciki”.
Ya kuma ƙara da cewa waɗanda za su ci gajiyar tallafin sun haɗa da fitattun mutane a jihar, ɓangarori daban-daban na tsofaffin masu riƙe da muƙaman siyasa, shugabannin jam’iyyar APC na jihar, ƙananan hukumomi da shugabannin mazaɓu na jam’iyyar da dai sauransu.
Hakazalika waɗanda za suci gajiyar Naira miliyan 300, 000,000 da Hon. Dr Aminu Sani Jaji ya bayar sun haɗa da tsofaffin masu riƙe da muƙaman siyasa a faɗin jihar, malaman Musulunci da masu karatun alkur’ani na kihar, Ƙananan hukumomi, da kuma Shugabannin mazaɓu na APC a faɗin Jihar.
Haka kuma za a miƙa wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a mazaɓu siyasa 147 da ke ƙananan hukumomi 14 na jihar gudummawar.
A cewar Aminu Sani Jaji, al’ummar mazabar sa na Ƙaura-Namoda da Birnin Magaji za su samu kaso na musamman na raguna da kuɗi.
