Fashewar bom ya halaka mutum tara a tashar Borno

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri

Rahotanni sun bayyana yadda fashewar bom ya kashe kimanin mutum tara a tashar mota a Ƙauyen Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala, Jihar Borno.

Bayanan da MANHAJA ta tattaro sun nuna cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Lahadi, yayin da kuma tashin bom ɗin ya raunata ƙarin wasu jama’a da dama a tashar.

Sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da harin; Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Hon. Abdulkarim Lawan, ya tabbatar faruwar lamarin, inda ya ce tashin bom ɗin ya rutsa da fasinjoji dake jiran mota.

Ya kara da cewa, wannan al’amarin abin Allah wadaran ne, wanda ya shafi al’ummar wannan kauyen, “Sun rasa rayukan su ne sakamakon tashin bam wanda aka dasa shi a inda suke jiran mota, a tashar mota dake kauyen Mairari.”

“Ina addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, ya sa aljannatul Firdausi ce makomar su, kuma ina fatan wadanda aka kai asibitin Monguno da Maiduguri, sakamakon raunukan da suka samu, su samu sauki.” In ji shi.

“Mutanen kauyen Mairari, a baya, shi ne kauyen da sau biyu mazauna garin suna yin gudun hijira a fadin karamar hukumar Guzamala, kuma ya taba kasancewa kifai; babu kowa saboda hare-haren Boko Haram/ISWAP.”

“Amma saboda juriyar jama’a, yawancin wadanda suka yi gudun hijira ne zuwa Monguno, Guzamala, da Maiduguri, su kan ziyarci kauyen Mairari don yin noma.”

Hon. Lawan ya yi kira ga sojoji da sauran hukumomin tsaro, su maida hankali wajen gudanar da ayyukan tsaro zuwa Guzamala, musamman a Gudumbali, shalkwatar karamar hukumar, kauyen Mairari, da sauran yankunan da Boko Haram ke cin karensu babu babbaka a yankin.

By Babaji