Shugaban ƙaramar hukumar Zamfara ya shaƙi iskar ‘yanci bayan kwana 61 a hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Nura Abdullahi, wanda shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a Jihar Zamfara, ya yi nasarar kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga bayan shafe kwanaki 61 a hannunsu.

Wata majiya daga iyalansa ta ce Hon. Abdullahi ya shaƙi iskar ‘yanci ne tare da wasu da aka yi garkuwa da su yayin harin. A ranar 25 ga Yuli ne aka ya awon-gaba da Abdullahi a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmake shi a gidansa da ke garin Bunguɗu.

An sako shi ne tare da wasu mutane, duk da cewa ba a bayyana ainihin yadda al’amarin sako sun ya kasance ba a nan take.

Haka kuma, Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Zamfara ba ta fitar da wani saƙo ba akan al’amarin yayin haɗa wannan rahoto.

By Babaji

Leave a Reply