NIMC ta ƙaryata zargin kutse cikin rumbun bayanai na NIN

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar kula da shaidar ƙasa ta Najeriya (NIMC) ta musanta wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa an yi kutse cikin rumbun bayanan lambobin shaidar ƙasa (NIN) na Najeriya. Hukumar ta bayyana ikirarin a matsayin ƙarya, tana mai cewa bidiyon wani tsohon rahoto ne da aka fitar a shekarar 2024, wanda tuni aka ƙaryata shi.

NIMC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Kayode Adegoke, ya fitar tare da wallafa ta a shafin hukumar na X ranar Alhamis. Hukumar ta ce babu wata matsala da ta shafi rumbun bayanan ƙasa, kuma ba a samu wata kutse ko satar bayanan da ke cikin tsarin ba.

Hukumar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da bidiyon da ke yawo, tare da dogaro da sahihan bayanai daga kafafen sadarwa na hukuma. NIMC ta kuma gargaɗi jama’a da su guji shafuka da manhajojin da ba su da izini waɗanda ke neman bayanan NIN, domin kare bayanan sirri daga masu amfani da su ba bisa ƙa’ida ba.

By ukarofi

Leave a Reply