
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Jihar Gombe, ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwanin ɗan takararta na gwamna a jihar. Wannan umarni ya biyo ƙorafin da Usman Aliyu Garry ya shigar wa kotun na ƙalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar a zaɓen 2027 da ke tafe.
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, wadda ta yi hukuncin, ta umarci PDP ta sake shirya sabon zaɓen fidda gwani bisa sharuɗɗa da dokokin jam’iyyar.
Garry ya ƙalubalanci zaman Pantami a matsayin ne bayan da PDP a ranar 26 ga Yuni, 2026 ta ayyana shi a matsayin ɗan takararta na zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a 2027, inda ya ce ba a bi hanyoyin da doka ta tsara ba wajen gudanar da zaɓen fidda gwanin.
Pantami, wanda a baya ɗan takara ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, ya koma PDP ne bayan APC ta zaɓi tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na sulhu. Daga bisani Pantami ya samu tikiti a PDP ta hanyar tabbatar da shi a matsayin ɗan takara yayin zaɓen fidda gwanin jam’iyyar wanda aka gudanar a watan Mayu.
Saidai, a hukuncin da aka gudanar a ranar Alhamis, Babbar Kotun ta umarci a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa biyayya ga sharuɗɗa da dokokin zaɓe. Hakan na zuwa ne bayan tsawon watanni na ƙalubalen shari’a wajen bin hanyoyin da suka samar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen na 2027.
