Shugaban ACF ya caccaki Afe Babalola kan kalaman ƙarfafa siyasar kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani jigo a Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Muhammad Alhaji Yakubu ya yi kakkausar suka ga wanda ya kafa kuma shugaban jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti, Cif Afe Babalola (SAN) kan cewa wanda ya fi kowa kuɗi, amma ba wanda ya fi kowa ba, zai yi nasara a zaven shugaban ƙasa mai zuwa.

An kuma ambato Babalola na cewa ɗan takarar shugaban asa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi ne ya fi cancanta da ya gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jigon ACF ɗin wanda kuma shi ne shugaban kiraye-kiraye na takarar Atiku/Okowa na zaɓen 2023 ya ce, furucin cin mutunci ne ga ’yan Nijeriya.

“Ina ganin Babalola a matsayin ɗan ƙasa mai daraja kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN) ya san cewa Nijeriya ba ta sayarwa ba ce. Ban yarda da shi ba kwata-kwata cewa wanda ya fi kashe kuɗi zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na Fabrairu 2023.

“Kuma tare da irin wannan sharhin, Mai Jami’ar da ake girmamawa yana aarfafa siyasan kuɗi wanda dokar zave ta ƙi.

“Kada ya manta cewa da duk wani abu da gwamnatin tarayya ta yi wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a shekarar 2015, Allah Madaukakin Sarki ya bai wa ’yan adawa mulki a lokacin.

Ina da yaqinin cewa tare da ficewar ’yan jam’iyyar APC daga hagu, dama da tsakiya zuwa PDP da kuma gazawar jam’iyyar mai mulki ta kowane fanni, Atiku zai ci nasara a gida da yardar Allah.

By Editor