Shugaban APC ya alaƙanta talauci da silar ta’addanci a Nijeriya 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana talauci a matsayin babbar matsalar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rashin tsaro a Nijeriya.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru 20 da lambar yabo ta ƙungiyar reshen jihar Filato a kasar Amurka (PSA-USA), wanda aka gudanar a ranar Laraba a birnin Lanham na jihar Maryland. Taron ya kasance mai taken “Rage talauci: Hanya zuwa zaman lafiya.”

Yayin da yake bayyana talauci a matsayin “dodo mai kai da ruwa” da gwamnati ke yaki da shi, Yilwatda ya koka da cewa kashi 63 na ‘yan Nijeriya a halin yanzu suna rayuwa cikin talauci mai ɗimbin yawa.

Shugaban jam’iyyar APC wanda ya samu wakilcin Dokta Patrick Dakum, ya jaddada cewa ba za a iya magance matsalolin tsaro da ƙarfi kaɗai ba, inda ya ce “kashi 30 cikin 100 na tsaro ya ta’allaƙa ne da aikin soja, yayin da kashi 70 cikin 100 ya dogara ne kan ilimi, kwarewa, da shugabanci na gari.

Ya yaba da ƙaddamar da Asusun Kamfen na R64 na Diaspora don tallafawa gyara da sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu a fadin ƙananan hukumomi 17 da unguwanni 64 a Jihar Filato.

A cewarsa, shirin “ba wai kawai ya samar da agaji ga ‘yan gudun hijirar ba ne kawai, amma kuma ya sake sabunta fata da kuma ƙarfafa kimar Nijeriya a gaban duniya.”

“Idan shekaru ashirin da suka wuce sun kasance game da rayuwa da ƙarfafawa, ashirin na gaba dole ne su kasance game da canji da tasiri. Wannan ƙungiya ba ta zama ‘yan kallo a cikin labarin Filato ba; mai ba da labari ne, “inji Shepkong, yayin da yake tunani game da tafiyar shekaru 20 na PSA-USA da kuma girmama waɗanda suka kafa ta, shugabannin da suka shuɗe, da kuma mambobin da suka tashi.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato, Naanlong Daniel, ya bukaci a kara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan majalisa da ‘yan kasashen waje domin ciyar da dokokin da suka shafi jama’a da zurfafa dimokuraɗiyya a jihar.

Uban Sarauta na Rana, HRH Miskoom Martin Shaldas III, ya yaba da juriyar ƙungiyar tare da jan hankalin membobin da su ci gaba da bayar da gudummawarsu ga ci gaban jihar.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a wannan biki shi ne ƙaddamar da asusun kamfen na R64 na Diaspora. Taron na kwanaki biyu ya kuma gabatar da baje kolin al’adu, zaman sada zumunta, da kuma bikin bayar da kyaututtukan karramawa a fannin ilimi, kasuwanci, hidimar jama’a, ayyukan jinƙai, da jagoranci na kasashen waje.

By ukarofi