Shugaban ICPC ya kafa tarihi a shari’ar kwangilar magani ta Kano

Spread the love

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN, ya kafa tarihi a matsayin shugaban hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya na farko da ya jagoranci ƙara a kotu da kansa.

Idan ba mu mance ba, yayin taron manema labarai lokacin da ake ƙaddamar da Dakta Aliyu ya yi alƙawarin bayar da gudummuwar sa wajen gabatar da wasu muhimman ƙararraki domin ƙarfafa aikin hukumar da kansa.

Da yake cika wannan alkawari, Dakta Aliyu ya gurfana a wata babbar kotu da ke Kano ranar Alhamis, inda ya wakilci ICPC a shari’ar da ta shafi zargin karkatar da kuɗaɗe da gwamnatin jihar Kano ta yi ta hannun shugabanninta na ƙananan hukumomi 44.

Waɗanda ake tuhumar da suka haɗa da kwamishinan ƙananan hukumomi da mataimakin gwamnan jihar, a baya sun ba da umarnin kotu na wucin gadi da ke hana ICPC gudanar da bincike, gayyata, ko kuma yi wa mutanen da ke da hannu a shari’ar da ake zargin ta yi musu tambayoyi.

A matsayinsa na shugaban ICPC na farko da ya bayyana a gaban kotu da kansa, Dr. Aliyu ya jaddada muhimmancin kasancewar sa. “Na zo nan ne domin in cika alkawarin da na yi na yin jagoranci da kaina. Wannan shari’ar tana da muhimmanci, kuma dole ne mu nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka,” inji shi.

Shari’ar dai ta ƙunshi ƙalubalantar hurumin hukumar ta ICPC, inda Waɗanda ake ƙaran suka ce sun samu umarnin kotu na dakatar da bincike daga bisani kuma suka shigar da ƙarar kotu. Dakta Aliyu, ya yi kakkausar suka kan halaccin muƙaman shugabannin riko, yana mai nuni da hukuncin kotun koli da ya haramta nada shugabannin riko a ƙananan hukumomi matukar ba a zabe su ta hanyar dimukraɗiyya ba.

By ukarofi