A ranar Asabar din da ta gabata ne kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC Ltd ya tura tankoki sama da 100 zuwa matatar Ɗangote domin lodin mai.
Kamfanin NNPC Ltd a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar ya bayyana cewa tara tankokin da aka yi a matatar man an yi ne domin fara lodin man fetur daga matatar.
“A shirye-shiryen da ake yi na jigilar man fetur daga matatar Ɗangote a ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, kamfanin NNPCL ya yi jigilar manyan motoci zuwa wuraren lodin man fetur na matatar da ke Ibeju-Lekki”
“Ya zuwa yammacin ranar Asabar, kamfanin NNPC Ltd. ya aika da manyan tankoki sama da 100, tare da wasu ɗaruruwa a kan hanya,” in ji NNPC Ltd.
