Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Musulman Nijeriya murnar zagayowar bikin mauludin Annabi Muhammad SAW.
Shugaban ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen koyi da kyawawan halaye da karantarwar Manzon Allah.
“Yayin da muke bikin mauludi, ya kamata mu yi duba kan irin rayuwar da Annabi Muhammad ( SAW) ya yi, wadda ke cike da tsarki, tausayi, kyautatawa da kuma jin ƙai, dole ne mu yi ƙoƙarin ganin mun yi koyi da waɗannan kyawawan halaye.” Inji shi.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci al’ummar Musulmi da su sadaukar da ranar mauludi domin yi wa ƙasa addu’a da kuma tausayawa juna.
