
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya sake tsarin atisayen da aka shirya gudanarwa a Zamfara a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta’adda.
Ya ce, atisayen sun ɗauki salo na kwamandanci inda janarorin kwamandodi za su yi aiki a matsayin kwamandodi na tawaga (component commanders).
Ya bayyana cewa, hakan na zuwa ne sakamakon yunƙurin inganta haɗin-gwiwa da kula a tsakanin jami’an tsaro.
Daraktan watsa Labarai na rundunar, Janar Tukur Gusau ya ce, shugaban tsaron ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyara wa gwamnan jihar, Dauda Lawal a ranar Juma’a.
Janar Gusau ya ce, shugaban ya ayyana sunan atisayen a matsayin ‘Operation Fansan Yamma’.
Ya kuma bayyana wa gwamnan jihar cewa an samo sauyin ne daga Hedikwatar tsaro na reshen jihar.
Ya ƙara da cewa, shugaban ƙasa ya amince da ƙara baza wasu jami’ai don samun kyakkyawar sakamako.
Kazalika, Janar Musa ya yi alƙawarin bai wa manoma kariya yayin gudanar da atisayen nasu da kuma kamo ƴan ta’addar da suka addabi yankin don su fuskanci hukunci dai-dai da laifukansu.
Bugu da ƙari, ya roƙi mutanen jihar kan kar su zama masu tsegumi ga ƴan ta’addar wanda a madadin haka, su ke bai wa jami’an tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen kai su ga nasara.
