Shugaban Kenya ya janye ƙudiri bayan mutane 22 sun mutu a tarzoma

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasar Kenya, William Ruto ya sanar da cewa zai janye ƙudirin ƙarin kuɗin haraji da ke ƙunshe da cece- kuce, bayan wata zanga- zangar da ta yi sanadiyar ƙona majalisar dokokin ƙasar a ranar Talata, 25 ga watan Yuni.

A wani jawabi da ya gabatar a kafar talabijin, shugaba Ruto ya ce, ba zai rattaba hannu kan ƙudirin dokar da ke tattare da ƙarin kuɗin harajin ba, matakin da ke nuna cewa ya bada kai bori ya hau.

A ranar Talata da ta gabata ce aka yi wata mummunar arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a Majalisar Dokokin Ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 23 tare da jikkata wasu da dama kamar yadda Ma’aikatan Lafiyar Ƙasar suka bayyana.

Shugaban ya ce, a yanzu zai fara tattaunawa da matasan ƙasar da ke jagorantar zanga-zangar don warware matsalolin da ke tsakaninsu, inda zai fara da ɗaukar matakin rage kasafin kuɗin fadar shugaban ƙasar.

“Na saurari muryoyin mutanen Kenya waɗanda suka yi babbar murya da cewa ba sa son wannan ƙudiri na ƙarin kudi na 2024, na kuma aminta da zaɓinsu. Saboda haka, ba zan sanya hannu kan dokar kuɗi ta 2024 ba, kuma daga baya za a janye shi,” inji shugaban a cikin jawabin da ya yi ta gidan talabijin.

Aƙalla mutane 22 ne aka kashe a zanga- zangar na ranar Talata, a cewar hukumar kare haƙƙin bil adama ta Kenya (KNHRC).

Masu zanga- zangar dai sun buƙaci ‘yan majalisar su kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da ƙudirin doka mai sanya sabbin haraji kan ƙasar da takaici kan tsadar rayuwa da ta shafe shekaru a ciki.

A ranar Talata, 25 ga watan Yuni, ɗaruruwan masu zanga- zangar sun kutsa shingen da ‘yan sanda suka kafa a wajen majalisar dokoki a Nairobi babban birnin ƙasar, inda ‘yan sanda suka yi ta harbe-harbe tare da yin ɓarna da yawa, a cewar Amnesty International Kenya.

Masu zanga- zangar sun shiga majalisar ne jim kaɗan bayan da ‘yan majalisar suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙudirin. ‘Yan majalisar sun gudu ta wani rami, amma rahotanni sun ce masu zanga- zangar sun bar ‘yan majalisar ‘yan adawa da suka kaɗa kuri’ar ƙin amincewa da ƙudirin ficewa daga ginin da aka yi wa kawanya.

Yayin da suke can, masu zanga- zangar sun lalata wasu ƙadarorin gwamnati tare da ƙona wani ɓangare na majalisar.

Da farko Mista Ruto ya mayar da martani ne da nuna rashin amincewa, inda ya ba da umarnin tura sojoji, yana mai cewa ba za a amince da “tashe- tashen hankula da rashin zaman lafiya ba.”

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, ya yi matuƙar baƙin ciki da rahotannin mace-mace da kuma jikkata, ciki har da ‘yan jarida da ma’aikatan lafiya da ke da alaƙa da zanga- zangar titunan Kenya.

Ya kuma buƙaci hukumomin Kenya da su daure, ya kuma yi kira da a gudanar da duk zanga- zangar cikin lumana.

By ukarofi