Shugabannin tsaro sun bayyana gaban Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH

Shugabannin fannin tsaro da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, sun bayyana a gaban Majalisar Wakilai domin tafka muhawara.

Jami’an sun haɗa da Shugaban Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa; Shugaban Rundunar Sojoji (COAS), Laftanal-Janar Taoreed Lagbaja; Shugaban Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar da kuma Shugaban Sojin Ruwa (CNS), Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Wannan na zuwa ne biyo bayan caccakar da jami’an suka sha daga ‘yan majalisar a makon jiya na tura wakilai da suka yi maimakon zuwa da-kai.

A makon da ya gabata ‘yan majalisar suka murtuƙe fuska na rashin zuwa zauren majalisar da kansu da jami’an suka yi wanda aka shirya yin zama da su a ranar Alhamis da ta gabata.

Maimakon haka, sai jami’an suka tura wakilai don su wakilce wajen amsa gayyatar majalisar, lamarin da bai yi wa majalisar daɗi ba.

Daga bisani Majalisar ta sake tsayar da Talata ta wannan makon a kan ranar da dole jami’an su bayyana da kansu a gabanta don tafka muhawara.