Babban Hafsan Tsaro bai mutu ba, yana cikin ƙoshin lafiya – Hedikwatar Tsaro

Daga BASHIR ISAH

Hedikwatar Tsaro da ke Abuja ta ƙaryata rahoton da ya ce Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya kwanta dama.

Da safiyar wannan Talatar wasu jaridu suka yaɗa rahoto kan cewa, Musa ya rasu.

Sai dai a martanin da ta mayar ta shafinta na X, Hedikwatar Tsaron ta ce rahoton ba gaskiya ba ne, don kuwa Babban Hafsan na raye kuma cikin ƙoshin lafiya.

“Saɓanin wani rahoton ƙarya da aka yaɗa, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, yana nan a raye kuma cikin ƙoshin lafiya,” in ji Hedikwatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, jama’a su zamo masu samun rahotanni daga sahihan kafofi masu yaɗa gaskiya.

A ranar 19 ga Yunin 2023 Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya.