Rasuwar Darakta Aminu Bono ta girgiza Gwamna Abba, cewar El-Mustapha

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna kaɗuwarsa bisa rasuwar fitaccen daraktan finafinan Hausa na Kannywood, Aminu S. Bono.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Sakataren Hukumar Tace Adabi na Jihar Kano, Abba El-Mustapha, wanda ya wakilce shi a wajen jana’aizar marigayin da aka gudanar ranar Talata, 21 ga Nuwamba, 2023, a maƙabartar Dandolo da ke birnin Kano.

A ganawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala jana’izar, Abba ya kuma bayyana Marigayi Bono a matsayin mutumin ƙwarai mai haƙuri da yakana tare da kyakkyawar mu’amula, wanda kuma ya kai ƙololuwa wajen fikira a sana’arsa.

Don haka ya ƙara da cewa, al’ummar Kannywood, Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya sun yi matuƙar asarar rashin wannan ɗa nasu.

Daga nan sai ya miqa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokan sana’arsa tare da bayyana yadda gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir ta tsuma da jin labarin rasuwar.

Darakta Bono, wanda ya shahara wajen bayar da umarni a Kannywood, musamman na waƙoƙi masu nishaɗantarwa, ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023, a birnin Kano, inda ya yi kwanan keso.

Ya bar mace ɗaya da kuma ’ya’ya uku.