Al’ummar Zamfara na da ƙwarin gwiwa kan gwamnatina, cewar Gwamna Lawal

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ce yana da yaƙinin al’ummar Zamfara na da ƙwarin gwiwa game da gwamnatinsa.

Lawal ya samu tabbacin hakan ne ganin yadda masoyansa a birnin Gusau suka fito don tarbarsa bayan da ya dawo daga ziyarar aiki a ranar Litinin.

Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce bisa la’akari da irin dandazon jama’ar da suka tarbi Mai Girma Gwamna, hakan manuniya ce game da ƙwarin gwiwar da al’ummar jihar ke da shi a kan gwamnatin jihar.

A cewarsa, gwamnatin Gwamna Lawal ta samu soyayyar al’ummar jihar waɗanda suka nuna cikakken goyon bayansu gare ta.

Ya ce, “Jiya, sa’ilin da ya dawo Zamfara daga ziyarar aikin da ya tafi a Abidjan, dandazon jama’a ne suka tarbi Gwamna Dauda Lawal.

“Jama’a sun tarbi ayarin motocin Gwamna Lawal ne tun daga yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe zuwa Gusau, babban birnin jihar.

“Da yake jawabi a Sakatariyar Jam’iyyar PDP, Gwamna Lawal ya jaddada cewa al’ummarm jihar Zamfara na da ƙwarin gwiwa a kan gwamnatinsa. Ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru don kyautata rayuwarsu.

“Ba mu fargabar a sake zaɓe. Al’ummar Zamfara sun ba mu amanar ƙuri’unsu. A shirye muke ko da kuwa gobe ne zaɓen. Mun shirya tafiya Ƙaramar Hukumar Maradun.

“Mun bada himma wajen ceto jiharmu, kuma babu wani abu da zai tsare mu wajen cimma ƙudirinmu,” in ji Gwamnan